Kungiyar Kwadago ta ?asa NLC ta mayar da martani kan jawabin ranar dimokuradiyya da shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi, inda ya bayar da tabbacin karin albashi mafi karanci ga ma’aikata, inda ya ce ya kasa bayar da kyautar da ake sa rai a ranar 12 ga watan Yuni.
Shugaban kungiyar ta NLC, Kwamared Prince Adewale Adeyanju wanda ya mayar da martani a madadin kungiyar ya ce mai yiwuwa shugaban kasar ya ba da labarin wasu sassa na tarihin tafiyar dimokuradiyyar mu daidai, amma a bayyane yake cewa an yi masa mummunar fahimta game da sakamakon da aka samu a tattaunawar albashi.
Ya ce suna sa ran shugaban kasar zai daidaita alkaluma biyu da kwamitin uku ya mika masa domin ma’aikata da talakawa, inda ya bayyana cewa da ya dace da kyautar ranar dimokradiyya.
shugaban kasar dai yace “Yayin da muke ci gaba da gyara tattalin arzikin kasa, zan rika sauraron jama’a kuma ba zan taba juya muku baya ba.
A cikin wannan ruhi, mun yi shawarwari cikin gaskiya kuma tare da bu?a??en hannu tare da ?ungiyoyin ma’aikata akan sabon mafi ?arancin albashi na ?asa. Nan ba da jimawa ba za mu aika da wani kudurin doka na zartarwa ga Majalisar Dokoki ta kasa don sanya abin da aka amince da shi a matsayin wani bangare na dokarmu na shekaru biyar masu zuwa ko kasa da haka.
