Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, gwamnatin tarayya karkashin shugaba Tinubu ta ?ora alhakin wahalar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki kan tsohuwar gwamnatin Shugaban ?asa Buhari.
Mai ba Shugaban ?asa shawara kan ya?a labarai Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa ya zamarwa tsohuwar gwamnati dole ta ?auki alhakin halin da ?an Najeriya ke ciki a yanzu.
Bayo Onanuga na mayar da martani ne kan wata ma?ala da jaridar New York times da ake wallafawa a Amurka ta fitar, da ke nuna irin yadda gwamnati mai ci ke yiwa ?an Najeriya matsar gya?a.
Ya ce rahoton babu komai a ciki illa kaidi na kafofin ya?a labaran ?etare, sai dai kuma abin takaici shine yadda suka kasa yin bayani kan yanayin da gwamnati mai ci ta kar?i ?asar a hannun gwmanitin Buhari da ta gabata.
Ya ce dukannin kafofin ya?a labarai dama ?an kasar na nunawa gwamnati yatsa kan yadda ta cire tallafin mai, sai dai an kasa gane irin asarar da ?asar ta shafe sama da shekaru 20 tana tafkawa a ?angaren bada tallafin man fetur ?in kuma ba’a samun sakamako mai kyau.
