Fina-Finai: Muna Shawartar ‘Yan Mata Masu Niyyar Shiga Harkar Fim Su Dakata – Maishadda

FB IMG 1718261711216~2

Labarin dake shigo mana daga birnin Kano na bayyana cewa daya daga cikin masu shirya fina-finai a arewacin najeriya Abubakar Bashir Maishadda yace, a kullum yana karbar kiraye-kiraye da sakonni sama da guda hamsin daga mata daban daban dake son shigowa kannywood da sunan zasuyi film, ni kaina nakan basu shawara su je suyi aure ko karatu, amma ni dai na daina daukan sabbin fuska acikin fina-finaina, sannan su kansu wadanda suke cikin masana’antar, a kullum addu’a na da fatana garesu shine, da sunyi film daya biyu sunyi suna, suje suyi aure abinsu, don shine darajar kowacce mace.

Maishadda dai shine mijin jaruma Hassana wanda tayi suna a fina-finan da maishadda ya shirya, da masu kamfanonin, daga cikin fina-finan da ta fito acikimsu sune kamar su HAUWA KULU, AGOLA, HAFEEZ da dai sauransu.

Mashiryin fina-finan ya maida martani ne, agabar da aketa tirka-tirka kan maganar da jaruma Hadiza Aliyu Gabon tayi na bawa mata masu son shigowa masana’antar shawara na cewa su hakura da shigowa masana’antar, acewarta sharrin dake cikinta yafi alherin dake cikinta yawa musamman idan ka kai kololuwa a shahara.

Related posts

Leave a Comment