Yakin Da Isra’ila Ke Yi A Gaza Ta’addanci Ne Fafaroma

FB IMG 1714121551442

Fafaroma Francis ya ce yana buga wa cocin Katolika da ke Gaza waya kullum domin sanin halin da mutanen yankin ke ciki. A cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CBS, Fafaroma ya ce daruruwan Falasdinawa da ke gudun hijira na fama da rashin abinci. Fafaroma ya ce a lokacin da aka kashe Uwa da ?arta a harabar cocin, rikicin ya tashi daga ya?i ya koma ta’addanci. Manyan mutane da ?ungiyoyi da dama dai na sukar ya?in da Isra’ila ke yi a Gaza.

Read More

Mun Shawo Kan Matsalar Dogayen Layuka A Gidajen Mai – NNPCL

images (18)

Kamfanin man fetur na ?asa NNPCL, ya ce ya shawo kan matsalar da ta jawo dogayen layuka a gidajen mai da ke fa?in ?asar. Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis, NNPCL ya ce an samu matsalar ne saboda “?awainiyar wajen jigilar man”. “NNPCL na tabbatar da cewa wahalar da ake sha wajen samun man fetur a wasu sassan Najeriya ta faru ne saboda matsalar da aka samu wajen jigilar man kuma yanzu an kawo ?arshen ta,” in ji sanarwar. Kamfanin ya ?ara da cewa ba shi…

Read More

Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa Sun Nemi Taimakon Amurka

IMG 20240426 WA0052

Gwamnonin wasu jihohin arewa maso yamma da maso tsakiyar Najeriya sun bukaci kasar Amurka ta taimaka musu wajen magance matsalar tsaro da ta addabi jihohinsu. Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce wajibi sun tinkarin wannan aiki tare domin kaucewa tufka da warwar. “Ina jin yaki da batun rashin bai daya zai taimaka, saboda idan muka kora ‘yan bindiga zasu koma jihar Zamfara amma idan a can Zamfara ana daukar irin wannan mataki lokaci guda can ma za a turo su, to da haka zamu magance lamarin baki daya”,…

Read More

An Rufe Rassan Bankin UBA Shidda A Jihar Kaduna

IMG 20240425 WA0037

Hukumar tattara ku?in shiga a jihar Kaduna ta rufe rassa shida na bankin UBA saboda zargin kaucewa biyan harajin naira miliyan 14. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai samamen ne bayan da hukumar gudanar bankin ta gaza mutunta takardun da aka aike masu. Tawagar hukumar, bisa jagorancin sakataren hukumar gudanarwa da mai bai wa hukumar shawara kan shari’a, Barista Aysha Muhammad, ta rufe rassan bankin tare da tallafin jami’an tsaro. Barista Aysha ta ce “bisa sashe na 104 na dokar haraji, hukumar ta samu izinin kotu ta ?wace tare da…

Read More

Tsananin Zafi Ya Hallaka Sama Da Mutum 40 A Jihar Kano

IMG 20240229 WA0298

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa hukumomia jihar sun fitar da wasu jerin shawarwari ga al’umma kan yadda za su kare kansu daga yanayin da ake ciki na tsanani zafi. Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton ?aruwar zazza?i mai zafi da hukumomin lafiya a jihar suka danganta da ?aruwar yanayin da ka?awar busasshiyar iska. Bayanai na cewa irin wannan yanayi da aka shiga ya haifar da mutuwar mutum fiye da 40 sannan da dama suna cikin mawuyacin hali. Kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf…

Read More

Dakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno

IMG 20240308 WA0095

Dakarun Sojin Najeriya sun ce sun yi wa ma?oyar ‘yan ta’adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ?ananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno. Wata sanarwa da mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa ‘yan ta’ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu. Samamen na ha?in gwiwa tsakanin rundunar Operation Ha?in Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin ‘yan ta’ddan abin da ya tilasta wa da dama tserewa. Sai dai Gabkwet ya…

Read More

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kamfanin Jirgin Sama Na Dana

images (17)

Ministan sufurin jiragen sama Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana. Hakan na zuwa ne kwana ?aya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed da ke Legas. Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin. Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin umarnin ?a’idojin tafiyar da harkar sufurin jirage. Acikin wata…

Read More

Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Tsarin Karbar Bashin Kayayyaki Ga ‘Yan Najeriya

images 2024 03 14T070645.613

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ?addamar da kashin farko na tsarin kar?ar bashin kaya ga ?an ?asar. Bayanin hakan na ?unshe cikin sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan ya?a labarai, Ajuri Ngelale ya fitar. Tsarin zai bai wa al’umma damar inganta rayuwarsu ta hanyar samun bashin kayyaki inda za su ri?a biya sannu a hankali tsawon lokaci. Da tsarin, jama’a na iya sayen gidaje da motoci da samun ilimi da kiwon lafiya ta hanyar bashi, inda za…

Read More

Sukar Dattawan Arewa: An Kalubalanci Bello Matawalle Ya Nemi Gafara

Tsohon Sanata, Kabiru Marafa, ya bukaci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da ya janye kalamansa na bayyana kungiyar dattawan Arewa (NEF) a matsayin “Jidali” ga yankin Arewa da muranenta. Sanata Marafa, wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, ya bukaci hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. Marafa ya shawarci Matawalle wanda tsohon gwamnan jihar Zamfara ne da ya fito fili ya nemi gafarar dattawan yankin Arewa da daukacin ‘yan Arewa bis wa?annan kalamai na sa. ” A matsayina…

Read More

An Gano Gidan Gasa Biredin Kungiyar ISWAP A Jihar Borno

Dakarun sojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi da ?ungiyar masu tayar da kayar-baya ta ISWAP ke amfani da shi a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno. A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ?ungiyoyin ta’addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce ha?in gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF ne suka gano wurin gasa burodin yayin wani samame da suka kai ma?oyar ?an ta’addan ranar Lahadi. “Majiyoyi sun ce an lalata gidan burodin tare da ?wato kayayyaki…

Read More

Najeriya Ba Ta Yi Balagar Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ba – Baturen ‘Yan Sanda

IMG 20240227 WA0004(1)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sifeto Janar ?in ?an sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai ga ta kafa ?an sanda Jiha ba wanda gwamnoni a jihohi ke da iko da. Egbetokun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron tattaunawa kan kafa ‘yan sandan jiha wanda kwamitin majalisar wakilai kan duba kundin tsarin mulkin kasa ya shirya. Ya ce rundunar ?an sandan kasa ba ta amince da hakan ba, amma kuma ta na rokon Majalisar kasa ta duba…

Read More

Rashin Adalci Ne Ke Rura Wutar Ta’addanci A Najeriya – Amina Mohammed

IMG 20240415 WA0083

Matainakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed tace hanyar da za’a bi wajen yaki da ayyukan ta’addanci itace ta tabbatar da adalci a tsakanin jama’a da kuma jagoranci na gari. Mohammed ta yi kiran mayar da hankali a kan illar da ayyukan ta’addanci ke yiwa ‘yan mata da mata tare da matasa, inda ta bukaci taimakawa wadanda ta’addanci ya shafa. Amina Mohammed ta sanar da hakan ne a yayin taron lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro dake addabar Najeriya musamman yankin arewacin kasar da ya gudana a ?asar Amurka.…

Read More

Jiga-Jigan APC A Shiyyar Arewa Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Dakatar Da Ganduje

images 2024 03 06T195109.222

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu Amma jiga-jigan APC a Arewa ta Tsakiya sun bayyana cewa dama kujerar tasu ce, don haka suka roki Tinubu da NEC su maye gurbin da ?an yankinsu Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya sun goyi bayan dakatarwar da…

Read More

Ana Kashe Mutum 28 Da Yin Garkuwa Da 24 Kowace Rana A Najeriya

IMG 20240225 WA0030

Al?aluman dai na kunshe ne a cikin rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, masu bincike kan halin da tsaro ke ciki a Najeriya ya fitar. Rahoton ya nuna cewar adadin mutanen da ake kashewa a kowace rana ya zarce adadin wanda ake yin garkuwa da su a kasar daga tsakanin watan Janairu zuwa Maris. Ya kuma ce kashi 80 cikin dari na wadanda aka kashe da kuma kashi 94 na wadanda aka yi garkuwa da su, daga Arewacin kasar suka fito. Rahoton ya nuna cewar akalla…

Read More

Masu Zargin Uba Sani Kan Bashin El-Rufa’i Sun Jahilci Aikin Majalisa – Barista Ibrahim Bello

IMG 20240421 WA0094~2

An bayyana cewa dukkanin jama’a da ke zargin Gwamnan jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani da cewa da goyon bayansa tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya ciyo bashin da ake bin jihar, sun jahilci aikin majalisa. Mataimaki na musamman ga Gwamna Uba Sani kan harkokin Masarautu Honorabul Barista Ibrahim Bello Rigachikum ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna. Barista Ibrahim Bello wanda tsohon ?an majalisar tarayya ne mai wakiltar karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ya ?ara da cewar…

Read More

Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Sake Bankado Hujjojin Badakalar Dalolin Gandujen

images 2024 03 06T195109.222

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta gano sama da Naira Biliyan 50 na kudaden kananan hukumomi da Ganduje ya karkatar zuwa Dala Domin Badakalar da su” Muhuyi Magaji Rimingado, shugaban zartarwa na hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ya bayyana cewa hukumar ta yi nasarar bin diddigin sama da Naira biliyan 50 da tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya karkatar zuwa Dala Muhuyi Magaji ya bayyana haka ne a wani…

Read More

‘Yan Ta’adda Za Su Bude Sabon Gidan Rediyo A Najeriya

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewa kungiyar ISWAP ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude sabon gidan rediyo na musamman. Kungiyar ta shirya bude gidan rediyon ne a yanar gizo mai suna “Radio Raeed” domin ya?a manufofinta. ‘Yan ta’addan ISWAP za su samar da gidan rediyo domin wayar da kan Mutane. ISWAP ta ce za ta yi amfani da gidan rediyon domin shawo kan jama’a shiga kungiyar musamman a yankin Arewa maso Gabas. An ruwaito cewa gidan rediyon zai kasance a Kangarwa wanda zai…

Read More

Najeriya Za Ta Karbi Bashin Dala Biliyan 2.2 Daga Bankin Duniya

images 2024 03 14T070645.613

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin tarayya na shirin karbar kusan dala biliyan 2.2 daga bankin duniya Ministan Kudi, Wale Edun ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen ayyukan Najeriya a taron bazara na Bankin Duniya/International Monetary Fund a birnin Washington DC na kasar Amurka A Jiya Asabar. Da yake magana kan hanyoyin samar da kudade na kasa da kasa ga tattalin arzikin Najeriya, Edun ya lissafa kudaden da kasashen waje ke aikawa da su waje, da…

Read More

Tinubu Zai Jagoranci Taron Yaki Da Ta’addanci Na Afirka A Abuja

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai bu?e taron ya?i da ta’addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ?asar. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron – wanda Najeriya da ha?in gwiwar ofishin ya?i da ta’addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya – za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu. Manufar taron ita ce ?arfafa ha?in gwiwa don ya?i da ta’addanci a ?asashen…

Read More

Ruftawar Kasa Ta Hallaka Yara Takwas A Jihar Kebbi

IMG 20240421 WA0047

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kebbi na bayyana cewa kimanin yara takwas sun mutun bayan ?asar gini ta rufta musu a maha?ar ?asar ginin ta Dustin Dukku da ke unguwar Badariya a ?aramar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi. Shugaban ?aramar hukumar Hon. Muhammad Dahiru Ambursa, ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka fara shirye-shiryen yi wa yaran jana’iza. Ya kuma ce akwai wasu ?arin yara biyu da suka jikkata ciki har da wanda ya karye a ?afa. To sai dai wani mutum da…

Read More