Jiga-Jigan APC A Shiyyar Arewa Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Dakatar Da Ganduje

images 2024 03 06T195109.222

Masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu Amma jiga-jigan APC a Arewa ta Tsakiya sun bayyana cewa dama kujerar tasu ce, don haka suka roki Tinubu da NEC su maye gurbin da ?an yankinsu

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya sun goyi bayan dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa na Riko, Dakta Abdullahi Ganduje. Sannan sun bu?aci cewa kujerar shugaban APC na ?asa wadda Abdullahi Adamu ya ri?e a baya ta koma shiyyarsu watau Arewa ta Tsakiya.

Jiga-Jigan jam’iyya mai mulkin sun bayyana cewa dama tun asuli ?a?aba Ganduje aka yi a kujerar shugaban jam’iyya na Riko, wanda hakan ya sa?a wa tsarin daidaito

Ana cikin tirka-tirka kan haka ne ranar Lahadi, wani tsagin APC a gundumar Ganduje, wanda ya yi ikirarin shi ne halastacce, ya tabbatar da dakatar da tsohon gwamnan, rahoton Leadership.

Da yake mayar da martani a Abuja, wani jagoran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya, Muhammad Etsu, ya ce suna goyon bayan dakatarwar.

Etsu ya kara da cewa dama kuskure ne APC ta maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu, wanda ya fito daga yankinsu da Ganduje dan Arewa maso Yamma. Ya kuma ro?i shugaban ?asa, Bola Ahmed Tinubu da kwamitin zartaswa na APC ta ?asa su amince da dakatar da Ganduje, kana su dawo da kujerar yankin Arewa ta Tsakiya.

“Muna kira ga dukkan shugabannin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki da su marawa kudurin Arewa ta tsakiya baya. “Hakan zai karawa jam’iyyar karfi, da hadin kai wanda zai share fagen samun ci gaba da fa?a?a karfin jam’iyya a dukkan sassan ?asar nan.”

Related posts

Leave a Comment