Dakarun sojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi da ?ungiyar masu tayar da kayar-baya ta ISWAP ke amfani da shi a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.
A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ?ungiyoyin ta’addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce ha?in gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF ne suka gano wurin gasa burodin yayin wani samame da suka kai ma?oyar ?an ta’addan ranar Lahadi.
“Majiyoyi sun ce an lalata gidan burodin tare da ?wato kayayyaki da suka kunshi manyan injunan bayar da hasken wutar lantarki guda biyu, wani abin gasa burodi da kuma wasu kayan ha?i da ake yin burodi da dama,” kamar yadda Makama ya ruwaito.
A cewar rahoton, gano wurin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka kai wani samame na tsawon mako ?aya da zimmar kakka?e ?an ta’dda daga yankunan da suka fi karfi a dajin Timbuktu Triangle, da sauran yankuna da suka ha?a da Talala, Ajigin, Dusula, Abulam da kuma Gorgi – wa?anda suka kasance wurare masu ha?ari da ?ungiyoyi masu tsattsaurar ra’ayi ke zama.
“Wa?annan ?ungiyoyin ?an ta’dda yawanci su ke da alhakin kai hare-hare, kwantan-?auna, binne abubuwan fashewa a kan hanyoyin Damboa, da Damaturu-Maiduguri, kai hare-hare garuruwan Askira, Buratai, Buni Yadi, da kuma lalata layukan wutar lantarki da ke ha?a Borno da Yoba,” in ji Makama.
Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da aikin fatattakar ?an ta’ddan babu kakkautawa, duk da irin ha?ari da wasu yankuna ke da shi, musamman ganin sansanonin ?an ta’addan na cikin manyan dazuka da kuma binne abubuwan fashewa da suke yi kan hanyoyi da za su kai wurinsu.
