Kamfanin man fetur na ?asa NNPCL, ya ce ya shawo kan matsalar da ta jawo dogayen layuka a gidajen mai da ke fa?in ?asar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis, NNPCL ya ce an samu matsalar ne saboda “?awainiyar wajen jigilar man”.
“NNPCL na tabbatar da cewa wahalar da ake sha wajen samun man fetur a wasu sassan Najeriya ta faru ne saboda matsalar da aka samu wajen jigilar man kuma yanzu an kawo ?arshen ta,” in ji sanarwar.
Kamfanin ya ?ara da cewa ba shi da niyyar sauya farashin man, wanda tuni ‘yan kasuwa suka ?ara farashinsa a jihohi.
Lita ?aya ta man ta zarta N750 a Abuja babban birnin ?asar.
Tun daga farkon makon nan aka fara ganin layuka a gidajen mai a Abuja, inda matsalar ta bazu zuwa jihohi daga baya.
