Kaduna: Za A Kaddamar Da Shirin Hadakar Makarantu Kan Batun Tsaro

IMG 20240310 WA0186

Gwamnatin Jihar Kaduna zata hade wasu makarantun Sakandare dana firamare wajen guda da yawan su ya kai 359 dake yankunan da matsalar tsaro ta fi Kazanta a fadin Jihar. Manufar hakan shi ne tabbatar da cewar ko wane Yaro ya sami damar zuwa makaranta don samin ilimin daya da ce duk da kalubalen tsaro. Gwamnatin Jihar ta dauki wannan matakin ne bayan data sami rahoton raguwar alkaluman adadin Yaran da suke zuwa makaranta, saboda barazanar tsaro. Gwamnan Jihar Sanata Uba Sani ne yake bayyana haka ta bakin Shugaban ma’aikatan Gwamnatin…

Read More

Dan Bindigar Da Ya Addabi Arewacin Sokoto Ya Shiga Hannu A Nijar

FB IMG 1715069000807

Labarin dake shigo mana daga jihar Sokoto na bayyana cewa ?asurgumin ?an Bindigar nan da ya addabi yankin arewacin Sokoto Kachalla Mai Daji ya shiga hannu a jamhuriyar Nijar tare da Yaranshi masu kisa da kone Garuruwa tare da garkuwa da Mutane. A cikin shekaru fiye da Goma ?an Bindiga MAI DAJI Yaci Zarafin ?auyukan Gabashin Illela Kamar Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, ?an Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu Da Sauran Dukan ?auyukan ?asar GADA Da Sukayi Iyaka Da GABASHIN ILLELA Jihar Sokoto. Jami’an…

Read More

Dole ‘Yan Najeriya Su Hada Kai Wajen Yaki Da Ta’addanci – Babban Hafsan Soji

IMG 20240308 WA0095

Babban Hafsan Sojin ?asa Janar Christopher Musa a ranar Asabar a Abuja ya yi kira ga ?an Najeriya da su ajiye ?abilanci da addini tare da ha?a kai domin ya?ar masu son ganin bayan Najeriya. Da yake jawabi a taro karo na biyu na ?ungiyar tsaffin ?alibai na makarantun Sakandire na ha?in kai na ?asa USOSA, Musa ya ayyana ta’addanci a matsayin babban ma?iyin Najeriya. ” Najeriya na fama da ?alubale, muna bu?atar ?asa da ke cike da ha?in kai domin mu tunkari dukkanin matsalolin da muke fuskanta. “Dole Najeriya…

Read More

Fitinar ‘Yan Bindiga Ta Tursasa Jama’a Gudun Hijira A Jihar Neja

IMG 20240323 WA0041

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Neja na bayyana cewa zaratan Sojojin Najeriya da aka tura yankin Allawa cikin ?aramar Hukumar Shiroro ta cikin Jihar Neja, sun janye daga aikin da aka tura su na kakka?e ‘yan ta’adda. Sun janye ne bayan an kashe masu sojoji biyu, ta hanyar ?ana masu nakiya a ranar Laraba. Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Manjo Janar Mohammed Garba Mai Ritaya, ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa sojojin sabbin tura wa ne a wurin domin su da?ile hare-haren ‘yan ta’adda.…

Read More

Bama Goyon Bayan Kafa ‘Yan Sandan Jihohi – Miyyeti Allah

IMG 20240317 WA0065

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah cattle Breeders Association of Nigeria ( MACBAN) Baba Usman ya ce, kafa ‘yan sandan jihohi da wasu gwamnoni ke hankoro ba dole ya zama anyiwa Fulani adalci ba. Baba Othman Ngelzarma, ya ce yau Bafillatani a Najeriya ya zama saniyar tatsa idan ya shiga hannun jami’an tsaro don haka samar da yan sanda jihohi zai ?ara kawo nakasu na rashin samar da tsaro mai inganci. Dan haka bama goyon bayan Kafa yan sandan…

Read More

Satar Danyen Mai: Najeriya Na Asarar Naira Tiriliyan 1.29 Duk Shekara – Kakakin Majalisar Wakilai

IMG 20240307 WA0056

Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce Najeriya na asarar Naira tiriliyan 1.29 a duk shekara sakamakon satar mai, fasa bututun mai da sauran laifuka. Abbas Tajudeen ya bayyana cewa Najeriya tana asarar kusan gangar ?anyen mai 300,000 kowace rana saboda sata. Kakakin majalisar wakilan ya bayyana hakan ne ta hannun shugaban kwamitin tsaro na majalisa, Babajimi Benson, a wajen ?addamar da cibiyar horas da sojojin ruwa a Eleme, jihar Ribas a ranar Juma’a. Ya ce lamarin ya haifar da ?alubale ga rundunar sojojin ruwan Najeriya domin ta tashi tsaye…

Read More

Dakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno

IMG 20240308 WA0095

Dakarun Sojin Najeriya sun ce sun yi wa ma?oyar ‘yan ta’adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ?ananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno. Wata sanarwa da mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa ‘yan ta’ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu. Samamen na ha?in gwiwa tsakanin rundunar Operation Ha?in Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin ‘yan ta’ddan abin da ya tilasta wa da dama tserewa. Sai dai Gabkwet ya…

Read More

An Gano Gidan Gasa Biredin Kungiyar ISWAP A Jihar Borno

Dakarun sojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi da ?ungiyar masu tayar da kayar-baya ta ISWAP ke amfani da shi a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno. A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ?ungiyoyin ta’addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce ha?in gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF ne suka gano wurin gasa burodin yayin wani samame da suka kai ma?oyar ?an ta’addan ranar Lahadi. “Majiyoyi sun ce an lalata gidan burodin tare da ?wato kayayyaki…

Read More

Najeriya Ba Ta Yi Balagar Kafa ‘Yan Sandan Jihohi Ba – Baturen ‘Yan Sanda

IMG 20240227 WA0004(1)

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Sifeto Janar ?in ?an sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai ga ta kafa ?an sanda Jiha ba wanda gwamnoni a jihohi ke da iko da. Egbetokun ya bayyana haka ne a ranar Litinin a taron tattaunawa kan kafa ‘yan sandan jiha wanda kwamitin majalisar wakilai kan duba kundin tsarin mulkin kasa ya shirya. Ya ce rundunar ?an sandan kasa ba ta amince da hakan ba, amma kuma ta na rokon Majalisar kasa ta duba…

Read More

Rashin Adalci Ne Ke Rura Wutar Ta’addanci A Najeriya – Amina Mohammed

IMG 20240415 WA0083

Matainakiyar Sakatare Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed tace hanyar da za’a bi wajen yaki da ayyukan ta’addanci itace ta tabbatar da adalci a tsakanin jama’a da kuma jagoranci na gari. Mohammed ta yi kiran mayar da hankali a kan illar da ayyukan ta’addanci ke yiwa ‘yan mata da mata tare da matasa, inda ta bukaci taimakawa wadanda ta’addanci ya shafa. Amina Mohammed ta sanar da hakan ne a yayin taron lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro dake addabar Najeriya musamman yankin arewacin kasar da ya gudana a ?asar Amurka.…

Read More

‘Yan Ta’adda Za Su Bude Sabon Gidan Rediyo A Najeriya

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewa kungiyar ISWAP ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude sabon gidan rediyo na musamman. Kungiyar ta shirya bude gidan rediyon ne a yanar gizo mai suna “Radio Raeed” domin ya?a manufofinta. ‘Yan ta’addan ISWAP za su samar da gidan rediyo domin wayar da kan Mutane. ISWAP ta ce za ta yi amfani da gidan rediyon domin shawo kan jama’a shiga kungiyar musamman a yankin Arewa maso Gabas. An ruwaito cewa gidan rediyon zai kasance a Kangarwa wanda zai…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Yanka Wa Jama’a Harajin Zama Lafiya A Zamfara

IMG 20240421 WA0046

Rahotannin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa a yayin da ake cika kwanaki bakwai da ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya a garin Gidan Dan Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, maharan sun bukaci ragowar jama’ar garin su biya kudin fansar mutanen da ake garkuwa da su, kuma su biya wa garin harajin zama lafiya. ‘Yan bindigan da suka kai hari garin Gidan Dan-Zara na yankin karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara a makon da ya gabata, inda suka kona gidaje…

Read More

ECOWAS Ta Ware Dala Miliyan 25 Domin Yaki Da Ta’addanci A Najeriya Da Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin ?asashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ware dala miliyan 25 da zimmar ya?i da ta’addanci a ?asashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso. Ecowas ta tsara kashe ku?in ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ?ungiyar da ke Abuja yau Juma’a. Farfesar ta ce an ware miliyan hu?u daga cikin ku?in don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa. “Haka nan, Ecowas ta ware dala miliyan ?aya da zimmar daidaita rayuwar…

Read More

‘Yan Bindiga Na Dab Da Zama Tarihi A Najeriya – Ribadu

images (13)

Mai ba wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sanar da haka, lokacin da yake ganawa da manema labarai a Jami’ar Usman Dan Fodio dake Sokoto. Ribadu yace gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a shiyar arewa maso yammacin Najeriya, da zaran ta samu labari, kuma wannan na daga cikin nasarorin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu tun daga watan Yunin da ya gabata. Mai bada shawarar ya tabbatar da matsalolin tsaron da…

Read More

‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Sabon Hari A Jihar Kaduna

IMG 20240310 WA0186

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa wasu ‘?an bindiga sun kashe mutum uku a wani hari da suka kai wasu ?auyuka na ?aramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna. An ruwaito cewa ?an bindigan sun kai harin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024. Mazauna yankin sun bayyana cewa an hallaka mutum biyu a wani ?auye da ke kusa da Anguwar Tanko Dogon Sarki da ke ?ar?ashin maza?ar Kakangi a ?aramar hukumar Birnin Gwari da misalin ?arfe 9:00 na safe. ?an bindigan sun kuma…

Read More

Ku Harbe Duk Dan Dabar Da Ya Shiga Hannu – Umarnin Gwamnan Neja Ga Jami’an Tsaro

IMG 20240323 WA0041

Gwmnan jihar Neja, Umaru Bago, ya kafa dokar ta-baci saboda tabarbarewar tsaro a jihar, biyo bayan barkewar fa?ace-fa?acen ?an daba a babban birnin jihar, Minna. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin bawan Sallah da tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu ya shirya a gonarsa da ke Minna. Bago ya kara da cewa, ya umarci jami’an tsaro da su harbe duk wani dan daba da aka samu yana barazana ga zaman lafiya a jihar. Umarnin na gwamnan ya zo ne a daidai lokacin da ayyukan…

Read More

An Sace ‘Yan Makaranta 1,680 An Kashe 180 Cikin Shekaru 10 A Najeriya – UNICEF

IMG 20240226 WA0252

Binciken Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da cewa a tsawon shekaru 10 an sace ‘yan makaranta sama da 1680 a Najeriya Kwararriya a fannin sadarwa ta UNICEF, Susan Akila, ce ta fitar da bahasin yayin wani biki domin tinawa da ‘yan matan Chibok bayan shekaru 10 da sace su Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin Najeriya domin inganta tsaro a makarantun kasar Sama da ‘yan makaranta 1,680 ne aka sace tare da kashe kusan 180 a hare-haren…

Read More

Bamu Da Wani Shiri Na Daukar Fansar Kisan Da Jami’an Tsaro Suka Yi Wa Yaranmu – Sheikh Zakzaky

IMG 20240414 WA0032

Kungiyar IMN a Najeriya da aka fi sani da Shi’a ta ?aryata cewa za ta dauki mataki kan kisan ‘yan ?ungiyar. Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce babu wani shiri na dakar fansa kan abin da ya faru.W Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Isah Hassan Mshelgaro ya fitar a madadin kungiyar ta kasa. Kungiyar ta ce Sheikh Zakzaky ya kadu da samun sakon da ‘yan sandan ke yadawa kan shirin daukar matakin. “Muna son sanar da al’umma cewa babu wani shiri na daukar fansa…

Read More

Ayyukan ‘Yan Daba Na Kara Kamari A Kano

IMG 20240229 WA0298

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki ‘yan daba da ke kulle a jihar. Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar. Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati. Ya bayyana yawan ‘yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su. Har ila yau, gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin kubutar da…

Read More

Sama Da Mutum 2000 Ne Aka Kashe A Watanni Ukun Farko Na Shekarar 2024

IMG 20240225 WA0030

Wani rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting da ke Abuja ya fitar a makon nan ya nuna yadda ‘yan Najeriya 2,200 suka mutu sakamakon matsalolin tsaro sannan aka yi garkuwa da mutum 2,270. Rahoton ya alakanta kisan jama’a da hare-haren ‘yan ta’adda da masu satar jama’a da kuma ayyukan dakarun tsaro na gwamnati da na sa-kai. Shugaban kamfanin, Malam Kabiru Adamu ya shaida wa BBC cewa kaso fiye da 90 na alkaluman na mace-macen da sace-sacen duka a arewacin Najeriya musamman arewa maso yammaci. Ya kara da cewa a…

Read More