Dan Bindigar Da Ya Addabi Arewacin Sokoto Ya Shiga Hannu A Nijar

FB IMG 1715069000807

Labarin dake shigo mana daga jihar Sokoto na bayyana cewa ?asurgumin ?an Bindigar nan da ya addabi yankin arewacin Sokoto Kachalla Mai Daji ya shiga hannu a jamhuriyar Nijar tare da Yaranshi masu kisa da kone Garuruwa tare da garkuwa da Mutane.

A cikin shekaru fiye da Goma ?an Bindiga MAI DAJI Yaci Zarafin ?auyukan Gabashin Illela Kamar Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, ?an Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu Da Sauran Dukan ?auyukan ?asar GADA Da Sukayi Iyaka Da GABASHIN ILLELA Jihar Sokoto.

Jami’an Tsaron Jamhuriyar NIJAR Suka Kamashi a wani gari da ake kira Tsarnawa dake Cikin Kasar Nijar Lokachin Da Yayi Yun?urin Fita Da Shanu sama da Dari 200 daga Najeriya zuwa kasar ta Nijar.

Related posts

Leave a Comment