Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa wasu ‘?an bindiga sun kashe mutum uku a wani hari da suka kai wasu ?auyuka na ?aramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna. An ruwaito cewa ?an bindigan sun kai harin ne a ranar Talata, 16 ga watan Afirilun 2024.
Mazauna yankin sun bayyana cewa an hallaka mutum biyu a wani ?auye da ke kusa da Anguwar Tanko Dogon Sarki da ke ?ar?ashin maza?ar Kakangi a ?aramar hukumar Birnin Gwari da misalin ?arfe 9:00 na safe.
?an bindigan sun kuma kai hari ?auyen Rafin Gora mai tazarar kilomita biyu daga yankin Dogon Dawa da misalin ?arfe 7:00 na yammacin ranar, inda suka kashe wani mutum ?aya tare da yin awon gaba da wasu mutum bakwai.
Wani mamban ?ungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya tabbatar da faruwar harin na Anguwar Tanko Dogon Sarki. Ya kuma ?ara da cewa a wannan rana ?an bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane a ?auyen Tashar Kaji da ke ?ar?ashin maza?ar Kakangi a ?aramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
?an majalisa mai wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar harin na ?auyen Rafin Gora sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan sauran abubuwan da suka faru ba.
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ?an sandan jihar Kaduna ba, ASP Mansur Hassan, saboda bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.
