Bama Goyon Bayan Kafa ‘Yan Sandan Jihohi – Miyyeti Allah

IMG 20240317 WA0065

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah cattle Breeders Association of Nigeria ( MACBAN) Baba Usman ya ce, kafa ‘yan sandan jihohi da wasu gwamnoni ke hankoro ba dole ya zama anyiwa Fulani adalci ba.

Baba Othman Ngelzarma, ya ce yau Bafillatani a Najeriya ya zama saniyar tatsa idan ya shiga hannun jami’an tsaro don haka samar da yan sanda jihohi zai ?ara kawo nakasu na rashin samar da tsaro mai inganci.

Dan haka bama goyon bayan Kafa yan sandan jihohi.. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da wakilin jaridar ATP Hausa.

Related posts

Leave a Comment