ECOWAS Ta Ware Dala Miliyan 25 Domin Yaki Da Ta’addanci A Najeriya Da Nijar

Kungiyar raya tattalin arzikin ?asashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ware dala miliyan 25 da zimmar ya?i da ta’addanci a ?asashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso.

Ecowas ta tsara kashe ku?in ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ?ungiyar da ke Abuja yau Juma’a.

Farfesar ta ce an ware miliyan hu?u daga cikin ku?in don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa.

“Haka nan, Ecowas ta ware dala miliyan ?aya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta’addanci ya shafa, kamar ‘yan gudun hijira da kuma wa?anda aka ji wa rauni,” in ji ta cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.

Ta ?ara da cewa a 2023 ka?ai, Ecowas ta ba da tallafin dala miliyan 12.6 ga mutane sama da miliyan hu?u da ta’addanci ya shafa a yammacin Afirka.

Related posts

Leave a Comment