Babban Hafsan Sojin ?asa Janar Christopher Musa a ranar Asabar a Abuja ya yi kira ga ?an Najeriya da su ajiye ?abilanci da addini tare da ha?a kai domin ya?ar masu son ganin bayan Najeriya.
Da yake jawabi a taro karo na biyu na ?ungiyar tsaffin ?alibai na makarantun Sakandire na ha?in kai na ?asa USOSA, Musa ya ayyana ta’addanci a matsayin babban ma?iyin Najeriya.
” Najeriya na fama da ?alubale, muna bu?atar ?asa da ke cike da ha?in kai domin mu tunkari dukkanin matsalolin da muke fuskanta.
“Dole Najeriya ta ha?a kai domin ya?ar duk wani abu da ke son ganin bayanta. Da yawa daga cikin mutane basa bu?atar irin albarkar da muke samu a matsayin mu na ?asa.
“Dole mu kunyatar da su, ta hanyar aiki tu?uru a tare. Kuma zamu cigaba,” inji shi.
Musa wanda tsohon ?alibi ne a Kwalejin ilimi ta Sokoto ya bayyana cewa wasanni babban abu ne da ke kawo ha?in kai a tsakanin al’umma, sai ya yi kira ga ?an Najeriya da su samar da zaman lafiya gami da inganta zaman lafiya.
