Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bada Umarnin Garkame Shugaban EFCC

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotu ta yi umurnin garkame shugaban hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, a gidan gyara hali na Kuje kan kin bin umurninta.

Jaridar Daily Independent ta ruwaito cewa, an umurci Sufeto Janar na Yan Sanda da ya tabbatar da kama Bawa tare da tsare shi a gidan yari nan da kwanaki 14 masu zuwa har sai ya wanke kansa daga zargin da kotu ke yi masa.

Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, 6 ga watan Fabrairu, Justis R.O. Ayoola na babbar kotun jihar Kogi ya amince da bukatar da aka nema na garkame shugaban na EFCC saboda kin bin umurnin kotu.

An tattaro cewa Bawa ya saba umurnin da kotu ta bayar a watan Nuwamban 2022 lokacin da ta nemi ya aiwatar da bukatunta a shari’ar Ali Bello. Ali Bello ya maka Bawa a kotu kan kama shi da tsare shi ba bisa ka’ida ba, inda ya yi nasara a kotu.

Related posts

Leave a Comment