EFCC Za Ta Yi Gwanjon Kadarorin Barayin Gwamnati

Hukumar EFCC ta sanar da cewa a ranar 9 Ga Janairu za ta yi gwanjon wasu kadarorin da su ka ha?a da manyan gidaje, filaye da fulotan da ta ?wato daga yawancin ?arayin gwamnati da kuma mazambata.

Za a yi gwanjon kadarorin ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023, a dandalin taron yaye ?alibai na Jami’ar NOUN da ke ma?wautaka da Hedikwatar EFCC.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Haka nan kuma EFCC ta umarci dukkan masu son shiga neman sayen kadarorin ya aika wa hukumar da bu?atar sa a rubuce nan da ranar Litinin, 9 Ga Janairu, 2023 sannan a bi nan efcc.gov.ng

Idan ba a manta na, Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa dai tun a ranar 16 Ga Disamba ya sanar cewa nan ba da da?ewa ba hukumar sa za ta fara sayar da kadarorin da ta ?wato daga hannun ?arayin gwamnati a, fa?in ?asar nan.

Ya fa?i cewa za a koma sayar da kadarorin ne na gidaje, fulotai da filaye masu yawa bayan kammala sayar da motocin da aka ?wato daga hannun ?arayin gwamnati.

Related posts

Leave a Comment