Dangote Ya Bada Lakanin Maganin Talauci A Najeriya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar babban ?an kasuwa Aliko Dangote ya jajirce wajen ganin cewa an farfa?o da masana’antar sa?a a Najeriya. Da yake jawabi a taron shekara-shekara karo na 50 (AGM) na kungiyar masana’antun Najeriya (MAN) ya yi kira da a ?aure ‘yan Najeriya masu shigo da kayan masa?u daga ?asashen waje.

A cewar attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, yana da muhimmanci majalisar dokokin ?asar ta zartar da wata doka da za ta hukunta sayar da kaya kasar waje ta hanyar ?aure masu laifi ba tare da zabin biyan tara ba.

“Ga masana’antar sa?ar tufafi, na yi imanin ya kamata gwamnati ta tsara doka a Majalisar Dokoki ta ?asa da za ta sa duk wanda ya sayar da kayan sa?ar tufafi na ?asashen ?etare da aka haramta, dole ne ya fuskanci zaman gidan yari ba tare da ba shi za?in biyan tara ba.

“Ainihin abin da ke faruwa a masana’antar sa?ar tufafi ba tsadar wutar lantarki ba ne. Harkar sa?ar tufafi ba za ta yiwu ba idan kuka ba su wuta mai rahusa amma ana ci gaba da fasa ?wauri. “Abin da ke faruwa shi ne, kamfanonin ?asashen waje suna hanka?o da kayayyakinsu Najeriya.

“Shi ya sa ba na son shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Lokacin da kuke shigo da kaya, kuna shigo da talauci ne tare da fitar da wadata da guraben aikin yi.”

Dangote ya kuma ce ya kamata gwamnati ta yi amfani da karfin da ta tara domin aiwatar da dokar hana shigo da shinkafa a yunkurin kawo ?arshen fasa-?waurin da ake yi a Najeriya.

“?an shekarun da suka gabata, masana’antun sa?ar tufafi a da su ne suka fi yawan ma’aikata bayan gwamnatin tarayyar Najeriya.

“Yau kuma za a iya tura mutane gidan yari a Indiya saboda suna sayar da kayan sa?a na kasashen waje a ko’ina. Haka kuma, idan aka hana wani abu a Amurka misali, babu yadda za a yi a saka shi don a sayar da shi a cikin shago.

“Amma abin da ke hana aiwatar da manufofin gwamnatin Najeriya shi ne rashin tsarin siyasa na ganin mun aiwatar da wa?annan manufofin ko da wane ne ransa zai ?aci.

Related posts

Leave a Comment