Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Hana CBN Aiwatar Da Wa’adin Amfani Da Tsoffin Kudi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kotun ?olin ta tarayya ta dakatar da gamnatin Buhari daga aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun ku?in kasar.

A baya dai CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sake.

Jihohin arewacin ?asar uku ne dai da suka ha?ar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ?arar a gaban Kotun ?olin ?asar suna bu?atar kotun da ta hana Babban Bankin ?asar aiwatar da wa’adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, al?alan kotun bakwai ?ar?ashin jagaorancin mai shari’a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ?asar da sauran bankunan kasuwanci na ?asar daga aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun ku?in ?asar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ?asar sun jingine batun aiwatar da wa’adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu.

Da wannan hukunci dai yanzu ‘yan ?asar za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ?asar.

Related posts

Leave a Comment