Dalilin Da Ya Sa Nake Tikar Rawa Da Waka A Gidan Gala – Tahir Fagge

Shahararren Dan wasan kwaikwayo Mai Suna Alhaji Tahir Fagge ya Bayyana cewa Dole Ce ta Sanya shi fitowa a cikin wata Waka da aka Ganshi Yana taka rawa da wata yarinya awajen Wani Gala. Tahir Fagge yace ya shiga mawuyacin Hali sakamakon jarrabawa da Allah yayi Masa na Rayuwar Sa. “Yace ya kasance Cikin mawuyacin hali Kuma Babu yadda zaiyi sakamakon yadda wasu Mutane suka Gaza fahimtar halin da yake ciki na rashin lafiya. “Bani da kudin da Ake bukata a ASibiti Kuma sau dadama wasu mutane basa iya taimakon…

Read More

Kano: Kotu Ta Bada Umarnin Kama Mawaki Ado Gwanja

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar wata kotun shari’a ta umurci hukumar yan sanda ta damke sanannen mawa?i Ado Gwanja da wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan koyawa matasa rashin tarbiyya a kafafen ra’ayi da sada zumunta, wani jami’in kotun ya bayyanawa AFP ranar Alhamis. Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon jiya bayan lauyoyi sun shigar da kara inda suka bukaci hukunta Ado Gwanja da ire-irensa bisa wakokin rashin tarbiyya da daurawa a yanar gizo, jami’in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan.…

Read More

Har Yanzu Ban Samu Namijin Da Ya Yi Mini Ba – Jarumar Fina-Finai

Fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood, Bimbo Akinsanya wacce aurenta ya mutu lokacin tana da yaro mai wata uku a shekarun baya da suka gabata, tace ta mayar da hankali kan fim a yanzu fiye da batun aure. A tattaunawarta da jaridar Vanguard, tace tana kokarin ganin ta ba wa ‘danta lokacinta wanda hakan ke da matukar muhimmanci. Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, ta bayyana yadda take kula da ‘danta ita kadai ba tare da tallafin uban yaron ba. “Ba abun wasa…

Read More

An Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon A Kotun Shari’a Ta Kaduna

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta sanin ma’aikacin nan ?an shekara 48, Bala Musa, wanda ya yi ikirarin ta masa al?awarin aure. Jarumar wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ranar Talata, ta fa?a wa Kotun cewa ba ta san mutumin da ake magana a kan shi ba. Da take jawabi ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a harabar Kotun, Gabon ta musanta tuhumar da ake mata baki ?aya inda…

Read More

Magidanci Ya Maka Hadiza Gabon Kotu Saboda Kin Aurensa

Wani maigidanci mai kimanin shekara 48 ya maka jarumar fina-finan Hausa na Kannywood, Hadiza Gabon, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna saboda ta ki amincewa ta aure shi. Maigidancin, mai suna Bala Musa, wanda ma’aikacin gwamnati ne ya shaida wa kotun cewa sun jima suna soyayya da jarumar, bisa alkawarin za ta aure shi, amma ta ci gaba da yaudarar shi. Bala ya ce, “Ya zuwa yanzu, na kashe mata N396,000. Duk lokacin da ta tambaye ni kudi na kan kashe mata ba bata lokaci cikin fatan…

Read More

Fina-Finai: Gwamnatin Kaduna Za Ta Gina Fim Village

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar babban sakataren hukumar KADIPA na jihar Kaduna, Khalil Nur Khalil ya cigaba da kokarin ganin an gina kauyen shirya wasan kwaikwayo wato’Fim Village’. A wani jawabi da ya fito daga shafin KADIPA a dandalin Twitter a ranar Alhamis, an fahimci gwamnatin Kaduna tana nan a kan aikin ‘Film Village’ domin bunkasa rayuwar matasa. Khalil Nur Khalil ya hadu da wakilan KCTA, shugabar Fasaha Café, Joseph Ike, da fitacciyar ‘yar wasar kwaikwayo, Rahma Sadau a kan wannan shirin. Shugaban na KADIPA…

Read More

Na Yi Nadamar Shiga Rikicin Zango Da Ali Nuhu – BMB

Jarumin fina-finan Hausa, wanda furodusa ne kuma darakta, Bello Muhammad Bello, wanda aka fi sani da BMB, ya bayyana shirinsa na dawowa sana’ar fim da sauran abubuwa dangane da rayuwarsa ta ilimantarwa. A tattaunawar da Daily Trust ta yi da BMB, ya fara da gabatar da kansa inda ya ce: “Sunana Bello Muhammad Bello, an fi sani da General BMB. Ni furodusa ne, darekta ne, jarumi sannan mai rubuta labari kuma na tashi ne a cikin rayuwar musulunci a cikin garin Jos da ke Jihar Filato. Kuma na yi makarantar…

Read More

‘Ya’yan Sarkin Kano Na Neman Rayuwata – Tsohuwar Jarumar Kannywood

Tsohuwar jarumar Kannywood, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Ibrahim, na neman agajin ?ungiyoyin kare ha??in ?an’adam da sauran jama’a kan halin ha’ula’in da ta ke ciki Lokacin da ta ke fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood, sunan ta Maijidda Ibrahim, yanzu kuma Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero. Ta na ?aya daga cikin ?imbin mata ‘yan fim da su ka yi aure kuma su na zaune a gidan miji. Tsawon shekaru 21 kenan tun da tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da sunan Maijidda Khusufi saboda wani fitaccen…

Read More

Mutuwa Ta Dauke Jarumar Kudanci A Coci

Labarin dake shigo mana daga Jihar Enugu na bayyana cewar Likitoci a asibitin East Side a Jihar Enugu sun tabbatar da mutuwar jarumar fina-fina ta Nollywood, Chinedu Bernard. Ta yanke jiki ta fadi ne a yayin da ta ke aikin tsaftace coci na St. Leo the Great Catholic Church da ke rukunin gidajen Tarayya a jihar. Faston cocin, Rabaran Fada Uchendu Chukwuma, da wasu masu ibada a cocin, sun garzaya da ita asibitin a inda aka tabbatar ta rasu. A cewar wani rubutu da daya daga cikin masu aiki a…

Read More

Jaruma Ummi Rahab Za Ta Amarce

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar manuniya tana nuna cewa jarumi kuma mawaki sannan mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya na gab da auren jarumar da ke haska fim din, Ummi Rahab. A makon da ya gabata rade-radin ya karu bayan jarumar ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta na Instagram, inda ta kira shi da “Masoyinta kuma mijinta kuma Aljannarta.” A karkashin rubutun na ta kamar yadda Aminiya ta nuna, mutane sun dinga tsokaci iri-iri har Ali Artwork yana cewa: “Insha…

Read More

Almajiranci: Fati Slow Ta Goyi Bayan Sarkin Wa?a

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci. Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa. A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take…

Read More

Ina Kan Ra’ayina Na Sukar Masu Tura ‘Ya’ya Almajiranci – Nafisa Abdullahi

A rubutu da tayi a shafinta na Twitter mai suna @NafisatOfficial, ta ce: “Ya bayyana cewa wasu mutanen ba su ji dadin maganar da nayi ba, na cewa a daina haihuwar ‘ya’yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba. Eh, na san an ce ku yi aure ku hayayyafa, amma a ina aka ce ku haifa ‘ya’yan ku watsar da su?. “Kun cika son bada kariya ga abunda kuka san cewa ba daidai bane. Suna cewa wai in bari in yi aure kafin in tsoma bakina a cikin irin…

Read More

A Kasuwa Nake Ga Duk Mai Bukata – Momi Gombe

Shahararriyar Jarumar Finafinan Hausa Maimuna Abubakar wadda aka fi sani da suna Momi Gombe ta bayyana cewar a halin yanzu ba tada da wani buri wanda ya wuce yin aure da raya sunnar ma’aiki. Momi Gombe ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan Rediyon BBC Hausa ya yi da ita cikin shirin “Daga Bakin Mai Ita”. A cewar Jarumar tabbas ta ta?a yin aure ita Bazawara ce amma ba ta haihu, a halin yanzu a kasuwa nake ga dukkanin mai bukatar aure. Sai dai Jarumar ta ?aryata…

Read More

Jarumin Wasan Barkwanci Ya Yi Garga?in Sa Matan Da Aurensu Ya Mutu A Fim

Furodusa kuma mai wasan barkwanci na masana’antar Kannywood, Malam Habu wanda aka fi sani da Mazaje, ya yi kira da a daina sa duk wata jarumar masana’antar da ta yi aure, sannan aurenta ya mutu ta dawo masana’antar. A wani dan karamin bidiyo da ya fitar, Mazaje ya ce, “duk wani furodusa ya sake wata ta fito a aure ya saka ta a fim, ni babu abin da zan ce masa, sai wuta balbal.” Sannan ya rubuta a saman bidiyon cewa, “duk wata jarumar Kannywood da ta yiaure ta fito…

Read More

Mai Shadda Zai Angwance Da Jaruma Hassana Muhammad

Furodusa a masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeriya Bashir Abdulkareem Mai Shadda, zai angwance da amaryarsa jaruma Hassana Muhammad. Za a daura auren ne a unguwar Masallacin Murtala da ke Kano a ranar 13 ga watan Maris kamar yadda Maishadda ya sanar. “Ina farin cikin gayyatar masoya daurin aurena. Wadanda kuma ba za su samu damar zuwa ba, sai a taya mu da addu’a.” Mai Shadda ya rubuta a shafinsa na Instagram hade da katin gayyata a ranar Talata. Jaruma Hassana Muhammadu na daya daga cikin jaruman Kanyywood mata da…

Read More

Jarumin Nollywood Lari Williams Ya Mutu

Rahoton da muke samu yanzu daga masana’antar finafinan kudancin Najeriya na bayyana cewar Gogaggen jarumin masana’antar fina-finai ta Nollywood, Lari Williams ya mutu ya na da shekaru 81. Williams ya rasu ne a gidansa da ke Ikom a Jihar Cross River a jiya Lahadi, kamar yadda iyalinsa su ka sanar a wata sanarwa da su ka fitar a jiyan. Kafin rasuwar sa, marigayin ya shafe kusan shekaru hamsin yana fim a Nollywood, inda ya yi finafinai kamar su Village Headmaster, Ripples, Mirror in The Sun da wasu saura da dama.…

Read More

Jaruma Aisha Tsamiya Za Ta Amarce

Labari mai dadi da ke bayyana a masana’antar Kannywood shi ne batun auren fitacciyar jaruma Aisha Aliyu Tsamiya. Majiyoyi masu yawa sun tabbatar da cewa za a daura auren a ranar Juma’a. Shafin Labaran Kannywood na Twitter ya fara wallafa labarin amma sai dai sun sanar da cewa jita-jita ce babu tabbaci. “Mun samu jita-jitar cewa a ranar Juma’ar nan mai zuwa jaruma Aisha Tsamiya za ta amarce… Kuma angon nata babban mutum ne.” A karon farko, mun ci karo da wallafar jarumi Ali Nuhu inda ya saka hoton jarumar…

Read More

Dalilin Da Ya Sa Nake Yi Wa Matan Kannywood Nasiha – Mai Sana’a

Shahararren ?an wasan barkwancin nan na masana’antar Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa mai sana’a ya bayyana dalilin da ya sa shi yawan yin nasiha ga ‘yan matan Fim. A zantawarshi da sashin hausa na gidan Rediyon Amurka ya bayyana cewar dukkanin kalamansa yana yin su ne bisa kishi da kuma inganta sana’ar su ta wasan kwaikwayo. Wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta ya nuna Musa Mai Sana’a na yi wa wasu mata ‘yan Hausa fim nasiha da gargadi akan yadda ya kamata su…

Read More

Dalilin Da Yasa Na Ba Fati Slow Kyautar Miliyan Guda – Sarkin Waka

A Kwanakin baya ne dai aka ji shahararren mawaki kuma ‘dan wasan nan, Naziru M. Ahmed ya yi wata kyautar da ta ba yawan al’umma mamaki inda ya ba da kyautar Miliyan biyu ga dattijuwa Ladin Cima sannan ya kuma bada miliyan guda ga jaruma Fati Slow. A wata hira ta musamman da Tambarin Hausa TV ta yi da Naziru M. Ahmed, an nemi a ji daga bakinsa, abin da ya sa ya ba Fati Slow kyautar kudi. Alhaji Naziru Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya bayyana…

Read More

Zina Da Mata Kafin Saka Su A Fim Gaskiya Ne – Jarumin Kannywood

Wallahi kannywood kaso 90 mazinata, ne kuma maganar zina da mace kafin a saka ta fim, Wallahi, Wallahi gaskiya ne. Domin shekera ta biyar a masana’antar fim, duk wata tsiya da ake na sani. Bana mantawa akwai wata da ta zo a saka ta a fim a shekarar 2007 aka ce mata za ta fito sau 9, amma duk scene daya sai an buga ta da kasa kuma ta yarda. Daga karshe ma aka ki saka ta aka bar ta da jinya. Haka kuma akwai wata buzuwa da ta zo…

Read More