Dalilin Da Ya Sa Nake Tikar Rawa Da Waka A Gidan Gala – Tahir Fagge

Shahararren Dan wasan kwaikwayo Mai Suna Alhaji Tahir Fagge ya Bayyana cewa Dole Ce ta Sanya shi fitowa a cikin wata Waka da aka Ganshi Yana taka rawa da wata yarinya awajen Wani Gala.

Tahir Fagge yace ya shiga mawuyacin Hali sakamakon jarrabawa da Allah yayi Masa na Rayuwar Sa.

“Yace ya kasance Cikin mawuyacin hali Kuma Babu yadda zaiyi sakamakon yadda wasu Mutane suka Gaza fahimtar halin da yake ciki na rashin lafiya.

“Bani da kudin da Ake bukata a ASibiti Kuma sau dadama wasu mutane basa iya taimakon ka Idan kashiga Wani Hali, Kuma basa binciken dalilin da yasa Kayi Wani abu.

“Haka Kuma Wani lokaci mutane basa binciken damuwar da yasa Kayi Wani abu, acewar jarumi Tahir Fagge

“Ya Cigaba da cewa wallahi hatta kudin magani da Ake nema a ASibiti bani da shi Kuma kudin gaba daya Basu Gaza naira dubu Dari da hamsin ba.#150,000.

“amma dai mawaki Rarara ya bani naira dubu ashirin sai Bashir Mai shadda dubu ashirin sai Abdul amart dubu ashirin.

“Ina cikin wanann yanayi wasu suka sameni cewa Ina Daga Cikin Bakin da zasu Halacci wannan wasa Kuma nan take suka bani naira dubu Dari da hamsin.

“Babu yadda zanyi Gashi bani da kudin sayen maganai Hakan yasa na yadda naje na Nuna musu yadda zasu tsara rawar.

“To Amma Kuma mutane suka Rika yadawa ana tsinemin ana zagina batare da sanin halin Rayuwa da yasa nayi Hakan ba acewar Tahir Fagge.

“Yace duk wadanda suka zageshi da tsine Masa ya yafe musu saboda yasan Basu San halin da ya shiga ba Kuma yayi musu uzuiri Kuma Shima ya nemi ayi Masa uzuiri

“Yace kaddara Ce ta sameshi Kuma tana kan kowa don Haka yayi kira ga mutane su rika taimamawa mutane ba sai sun nemaba acewar Sa.

“Tahir Fagge yayi Wanann bayani ne yayin zantawar Sa da Sashin Hausa na BBC ta cikin Shirin Daga Bakin Mai ita.

Related posts

Leave a Comment