An Gurfanar Da Jaruma Hadiza Gabon A Kotun Shari’a Ta Kaduna

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, ta musanta sanin ma’aikacin nan ?an shekara 48, Bala Musa, wanda ya yi ikirarin ta masa al?awarin aure.

Jarumar wacce ta bayyana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari Kaduna ranar Talata, ta fa?a wa Kotun cewa ba ta san mutumin da ake magana a kan shi ba.

Da take jawabi ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, a harabar Kotun, Gabon ta musanta tuhumar da ake mata baki ?aya inda tace zargi ne mara tushe ballantana makama.

“Bayan ta saurari zargin da ake mata, jarumar ta yi nata jawabin wanda a cewarta, ba ta ta?a ha?uwa da shi ba, bama ta san abun da ya faru ba. “Saboda haka ba mu san abin da yake ikirari ba, bai dame mu ba, mun kuma saurare shi, yanzu mun bar kotu ta yanke hukunci.”

A ?aya bangaren, lauyan wanda ya shigar da ?ara, Barista N. Murtala, ya ce wanda yake karewa ya ha?u da Gabon a Facebook, daga nan suka zama abokai. Ya ?ara da cewa ta yi al?awarin zata aure shi shiyasa yafara kashe mata ku?i ba tare da jin komai ba.

Daga nan, Al?alin Kotun Mai Shari’a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ?age zaman zuwa ranar 28 ga watan Yuni, 2022. Ya kuma bai wa Jaruma Hadiza Gabo beli bisa shara?in zata gabatar da masu tsaya mata kuma mazauna cikin garin Kaduna.

Related posts

Leave a Comment