Dalilin Da Ya Sa Nake Yi Wa Matan Kannywood Nasiha – Mai Sana’a

Shahararren ?an wasan barkwancin nan na masana’antar Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa mai sana’a ya bayyana dalilin da ya sa shi yawan yin nasiha ga ‘yan matan Fim.

A zantawarshi da sashin hausa na gidan Rediyon Amurka ya bayyana cewar dukkanin kalamansa yana yin su ne bisa kishi da kuma inganta sana’ar su ta wasan kwaikwayo.

Wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta ya nuna Musa Mai Sana’a na yi wa wasu mata ‘yan Hausa fim nasiha da gargadi akan yadda ya kamata su taka a sannu a harkar domin makomar rayuwarsu.

Sana’ar Hausa Fim dai na fuskantar suka da tsangwama daga jama’a biyo bayan kallon da ake yi musu a matsayin masu bata tarbiyya.

Related posts

Leave a Comment