Jaruma Ummi Rahab Za Ta Amarce

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar manuniya tana nuna cewa jarumi kuma mawaki sannan mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya na gab da auren jarumar da ke haska fim din, Ummi Rahab.

A makon da ya gabata rade-radin ya karu bayan jarumar ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta na Instagram, inda ta kira shi da “Masoyinta kuma mijinta kuma Aljannarta.”

A karkashin rubutun na ta kamar yadda Aminiya ta nuna, mutane sun dinga tsokaci iri-iri har Ali Artwork yana cewa: “Insha Allah.” Wani Murtala Bloko ya ce: “Wanda ba zai iya gani ba ya kau da idonsa.” Wani Real Adam M Ibrahim ya yi tsokaci inda ya ce: “Dan bakin ciki sai ya mutu, amma fa ban kama suna ba.”

Duk da dai ana zargin an yi maganganu da habaicin da Adam Zango ne, amma kuma abin mamakin shi ne har da Murtala Bloko wanda na hannun daman Adam din ne.

A kwanakin baya an samu sabani mai yawa tsakanin Adam A. Zango, wanda tsohon Uban gidan Ummi Rahab ne, da jarumar wanda maganganu suka dinga tashi iri-iri.

Ana zargin ya nemi soyayyar jarumar ne amma kuma sai ta ki amincewa wanda hakan ya rura wutar rikicin. Abin lura anan shi ne yadda yanzu haka jarumar ta ke fitowa a kusan duk wakokin Lilin Baba da fim dinsa.

Related posts

Leave a Comment