A Kwanakin baya ne dai aka ji shahararren mawaki kuma ‘dan wasan nan, Naziru M. Ahmed ya yi wata kyautar da ta ba yawan al’umma mamaki inda ya ba da kyautar Miliyan biyu ga dattijuwa Ladin Cima sannan ya kuma bada miliyan guda ga jaruma Fati Slow.
A wata hira ta musamman da Tambarin Hausa TV ta yi da Naziru M. Ahmed, an nemi a ji daga bakinsa, abin da ya sa ya ba Fati Slow kyautar kudi.
Alhaji Naziru Ahmed wanda aka fi sani da Sarkin Waka ya bayyana dalilin da ya sa ya maida sharri da alheri. Fitaccen mawakin yake cewa ya tashi daga barci sai ya ji ana ta magana a game da kalaman da Fati Slow tayi, har ana ba shi shawarar ya kai kara.
Mawakin ya bayyana cewa abokansa da suke aikin lauya sun yi masa maganar cewa a shiga kotu. An wallafa bidiyon hirar a shafin Facebook da sauran kafafen sadarwa na zamani.
A nan ne sai ya ce wani hadisin Manzon Allah Muhammad (SAW), ya bijiro masa, wanda da shi ya yi amfani, ya ba jarumar wasan kwaikwayon kyauta. Gundarin wannan hadisi na Annabi SAW yana cewa: “Ku ji tsoron Allah SWT a duk inda ku ka samu kan ku, ku biyo aikin sharri da na alheri, na alherin zai shafe sharrin, ku mu’amulanci mutane da kyakkyawan dabi’a.”
Abu Dharr da Mu’adh Jabal suka ji wannan hadisi daga bakin Annabi SAW. Tirmidhi ya inganta hadisin a littafinsa.
An gayyaci mawakin ne a shirin AmonGaskiya wanda aka saba yi a wannan gidan talabijin. Wasu daga cikin wadanda suka saurari hirar a shafin Facebook sun rika yabawa mawakin, su na cewa: Naziru Sarkin Wa?a Allah yayi maka albarka ya kara daukaka da juriya da jajircewa wajen fadar gaskiya da kuma neman yadda za’a kawo gyara.
Hakika duk me fadin gaskiya dole ya hadu da kalubale daga wadanda basu son gaskiya, son a dawwama akan rashin gaskiya shine yasa babu cigaba a kasa. Allah ya kara mana hakuri da tausayi da tunani mai amfani.
Daga bisani jaruma Fati Slow ta nemi gafarar Sarkin wakar bayan ta karbi kyautar kudin, wanda asalin rikicin ya samo asali ne bayan wata hira da BBC ta yi da Jaruma Ladin Cima.
