Kano: Kotu Ta Bada Umarnin Kama Mawaki Ado Gwanja

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar wata kotun shari’a ta umurci hukumar yan sanda ta damke sanannen mawa?i Ado Gwanja da wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan koyawa matasa rashin tarbiyya a kafafen ra’ayi da sada zumunta, wani jami’in kotun ya bayyanawa AFP ranar Alhamis.

Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon jiya bayan lauyoyi sun shigar da kara inda suka bukaci hukunta Ado Gwanja da ire-irensa bisa wakokin rashin tarbiyya da daurawa a yanar gizo, jami’in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan.

“Kotun Shari’ar ta bada umurni ga kwamishinan ‘yan sanda ya damke wadannan mutum 10 kuma a gudanar da bincike kan rawar da suka taka wajen bayyanawa rashin tarbiyya.” Ana zargin Ado Gwanja da sakin waka mai suna “A Sosa”. Amma kwanaki tara bayan da kotu ta bada wannan umurnin, har yanzu ba’a damkesu ba.

Related posts

Leave a Comment