Duniyar Fina-Finai: Jarumi Kumurci Ya Angwance

Labarin da muke samu daga birnin Kano na bayyana cewa bayan kusan shekaru ashirin da rasuwar rabin ransa, jaruma Balaraba Muhammad, jarumi Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya sake angwancewa. Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Ahmed Prince Gandujiyya ya wallafa hotunan a shafinsa. Gandujiyya ya shaida cewa Kumurci ya taba wani auren bayan jaruma Balaraba ta rasu amma Allah ya yi wa sabuwar amaryar rasuwa. Kamar yadda gandujiyya ya sanar: “Ango Sha’aibu Lawan (Kumurci) ya yi sabon aure tun bayan shekaru…

Read More

Sai ‘Yan Mata Sun Bada Kansu Kafin Ake Saka Su A Fim – Sarkin Waka

Shahararren mawakin zamani Naziru Sarkin Waka ya yiwa jagororin Hausa film wankin babban bargo, inda ya bayyana halayyar tsarin ‘yan jari hujja da danniya da lalata da akeyi a Masana’antar Naziru yace Wallahi ‘yan Hausa film ba Allah a ranku, ya fadi hakane sakamakon hiran da BBC tayi da wata tsohuwar jaruma a Masana’antar Hausa film Ladi Cima inda tace bata samun abinda ya wuce Naira dubu 10, shine sai daraktocin film suka mata caa suna raddi a gareta Sarkin Waka yace kamar Ali Nuhu da Falalu Dorayi karya suke…

Read More

Ban Taba Samun Dubu 10 A Sana’ar Fim Ba – Ladin Cima

Fitacciyar ?ar wasan Hausa, wadda ke fitowa a matsayin uwa ko kuma kaka a masana’antar Kannywood wato Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha’awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim saboda a zamanin babu gidan talabijin a Kano. Ladin Cima wadda ta bayyana haka a tattaunawa da gidan Rediyon BBC ta bayyana cewa ta soma fitowa a fim tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasaYakubu…

Read More

Ban Taba Samun Dubu 10 A Sana’ar Fim Ba – Ladin Cima

Fitacciyar ?ar wasan Hausa, wadda ke fitowa a matsayin uwa ko kuma kaka a masana’antar Kannywood wato Ladin Cima Haruna wadda aka fi sani da Tambaya, ta bayyana cewa ta soma harkar fim bayan rasuwar mijinta inda ta ce dama tun a baya tana da sha’awar fim din. Ta ce Kaduna suke zuwa su yi fim saboda a zamanin babu gidan talabijin a Kano. Ladin Cima wadda ta bayyana haka a tattaunawa da gidan Rediyon BBC ta bayyana cewa ta soma fitowa a fim tun zamanin mulkin tsohon shugaban kasaYakubu…

Read More

Gaskiyar Magana Kan Mutuwar Auren Ado Gwanja

Majiyar mu ta Idon Mikiya da Shafin Labarai na Hausa tace wani labari da muke samu marar da?in ji, akwai ?ishin-?ishin ?in cewa mawa?i Ado Gwanja ya saki matar sa Maimuna, inda a wani bincike da Tashar YouTube ta Tsakar Gida ta gudanar ta gano cewa mawa?in ya sauwakewa matar tashi, kuma sakin ba daya ba har saki uku. Tashar Tsakar Gida sun tambayi dalilin sa?anin da ya haddasa sakin da tsawon lokacin da aka yi da yin sakin ba su samu wani gamsashshen bayani ba, amma dai sun tabbatar…

Read More

Kotu Ta Bada Umarnin Iza Keyar Jaruma Sadiya Haruna Kurkuku

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Kotun Majistire, da ke zaman ta a Filin Jirgin sama na Kano, ta yanke wa wata jarumar Kannywood kuma shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta instagram, Sadiya Haruna hukuncin ?aurin watanni shida. Kotun, ?ar?ashin jagorancin Mai Shari’a Muntari Dandago, ta yanke hukuncin ne ba tare da za?in tara ba. An yanke wa Sadiya wannan hukuncin ne bisa kalaman ?atanci da ta yi ga wani ?an wasan kwaikwayo na Kannywood, Isah I. Isah a shafinta na Instagram. An ruwaito cewa…

Read More

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bada Umarnin Kamo Jarumin Hausa Fim

Kotun shari’ar Musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a a Jihar Kano ta bayar da umarnin kamo mata Jarumin wasan Hausan, Sadiq Sani Sadiq. Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa wani mai shirya fina-finai, Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da ?arar a gaban kotun, inda ya ke ?orafin cewar ya baiwa jarumin ku?i domin ya yi masa aikin film, amma ya?i zuwa don yin aikin. Mai ?arar ya kuma yi ?orafin cewa ?in yi aikin da Sadiq ya yi ya ja masa asara mai yawa. Alkalin Kotun, Maishari’a Sagiru Adamu,…

Read More

Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Bada Umarnin Kamo Jarumin Hausa Fim

Kotun shari’ar Musulunci da ke Hotoro Masallacin Juma’a a Jihar Kano ta bayar da umarnin kamo mata Jarumin wasan Hausan, Sadiq Sani Sadiq. Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa wani mai shirya fina-finai, Aliyu Muhammad Hannas ne ya shigar da ?arar a gaban kotun, inda ya ke ?orafin cewar ya baiwa jarumin ku?i domin ya yi masa aikin film, amma ya?i zuwa don yin aikin. Mai ?arar ya kuma yi ?orafin cewa ?in yi aikin da Sadiq ya yi ya ja masa asara mai yawa. Alkalin Kotun, Maishari’a Sagiru Adamu,…

Read More

Naso Ace Dangote Ne Mahaifina – Mawakiya Tiwa Savage

Fitacciyar Mawa?iyar nan Tiwa Savage tace taso ace wanda yafi kowa ku?i a Afirka Aliko ?angote shine mahaifin ta. Savage ta bayyana haka a shafin ta na Snapchat a ranar Alhamis, inda ta bayyana ba?in ciki na yadda tasha wahala wajen yin ku?i.Tiwa Savage Ta rubuta; “ina da wani taro. Amma ba abune mai sau?i wajen yin ku?i. Allah ne ya taimake ni, amma miyasa Babana bai zama ?angote ko kuma wani kamar haka. Mahaifiyar mawa?iyar ta mutu a ranar 19 ga watan Yuni na shekara 2021 an binne shi…

Read More

Mawaki Ali Jita Ya Bayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Kano

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na nuna cewa yayin da jama’a ke ci gaba da hasashen yadda babban zaben kasar na 2023 zai kasance, an gano wani fostan yakin neman zabe na shahararren mawakin nan na masana’antar shirya fina-finai na Kannywood, Ali Isa Jita. Fostan wanda abokiyar sana’arsa Rahama Sadau ta wallafa a shafinta na Instagram, ya nuna cewa mawakin zai fito takarar kujerar gwamnan jihar Kano ne a zaben na 2023. Sai dai kuma babu suna ko tambarin wata jam’iyyar siyasa a cikin hoton wanda ke dauke…

Read More

Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Fitar Fim Din Makaranta – Darakta

Daraktan fim din nan da ake ta yin tallansa mai suna ‘Makaranta’ ya ce bai damu da barazanar da hukumar tace fina-finan Jihar Kano ta yi na kama shi ba. Fim ?in Makaranta wani shiri ne da ya haifar da cece-kuce a ?an kwanakin nan bayan da a ka saki tallansa a kafafen sadarwa. Shi dai fim ?in an yi shi ne domin koya jima’i tsakanin matasa, inda a ka yi amfani da kalaman batsa da sauran rashin tarbiyya a cikin sa har ya sanya Hukumar Tace Finafinai ta Jihar…

Read More

Jaruman Kannywood Sun Nesanta Kansu Da Fim Din Badala

A daidai lokacin da labarin fim din Makaranta ya ke ci gaba da yamutsa hazo tare da yin tofin Allah tsine ga masu shirya fim din, sai ga shi Shugaban kungiyar Jaruman kannywwod Alhassan Kwalle ya fito ya nesanta kungiyar su da wannan fim din. A tattaunawar da Jaridar Dimukaradiyya ta yi da shi ya bayyana cewar. “Mu a matsayin mu na kungiyar Jarumai ba mu da wata Alaka da wannan fim din mai dogon zango da aka fara tallan sa a kafafen sada zumunta domin ba Yan kungiyar mu…

Read More

Fim Din Badala: Hukumar Tace Fina-Finai Na Neman Furodusa Ruwa A Jallo

A yanzu haka dai Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta baza komar ta wajen neman wani Furodusa wanda ya shirya wani fim na Badala mai suna Labaran Duniya, wanda tuni ya fara tayar da kura, tun daga lokacin da aka fara saka wani yanki na fim din a kafar sadarwar Social Media da sunan talla. Fim din dai yana nuni tare da koyar da harkar Badala tsakanin maza da maza da Kuma tsakanin Mata da Mata. Kan haka ne yasa mutane da suka ga tallan suka rinka yin tofin…

Read More

Ban Da Burin Da Ya Wuce Aure – Jaruma Fati Zinariya

Shafin Rumbun Nishadi na Jaridar Leardeship Hausa ya zakulo muku daya daga cikin fitattun Jaruman Kannywood wadda take haskawa a yanzu wato FATI MUHAMMAD ADAM wadda aka fi sani da FATI ZINARIYA ko HAJIYA SARAH cikin fim din Izzar so. Jarumar ta bayyana wa masu karatu babban burinta a rayuwa da kuma irin gwagwarmayar da ta sha wajen ganin ta shiga masana’antar Kannywood tare da sauran wasu batutuwan wanda suka shafi sana’arta ta fim ga dai tattaunawarta tare da YAKUBU FURODUSA: Masu karatu za su so su ji cikakken sunanki tare da dan takaitaccen tarihinki…

Read More

Dalilin Ficewata A Shirin Labarina – Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba. A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta. Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu…

Read More

Ba A Samun Daukaka Da Girman Kai – Jarumi Auwal Isa West

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Auwal Isah West, ya bayyana cewar akwai bambanci sosai a tsakanin jarumai na yanzu da kuma na baya. Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, Inda yake cewa na shafe tsawon lokaci sama da shekaru 20 a wannan masana’antar, wadda tunranda na shigo ina aikin tuka motar Tixi a lokacin ina daukar kaya idan za a tafi wajen lokeshin da haka na zo na zama jarumi don haka na sha Gwagwarmaya sosai. Sannan kuma duk wanda ka…

Read More

Ina Alfahari Da Masoyana – Jaruma Hafsat Hassan

Wata Sabuwar jaruma a Masana’antar Kannywwod Hafsat Hassan ta nuna yadda take jin dadin ta a game da irin kaunar da mutune su ke nuna Mata tun daga lokacin da suka fara ganin ta a cikin shirin fim. Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya da muka tambaye ta irin yadda ta ke gudanar da rayuwar ta a matsayin ta na Sabuwar jaruma sai ta ke cewa. “To a gaskiya duk da ban dade da fara shirin fim ba, Ina alfahari da ita saboda alamun nasara da…

Read More

Bamu Da Burin Da Ya Wuce Yin Aure – Tagwayen Shirin Dadin Kowa

Jaruman shirin Dadin Kowa Hassana Yusuf da Hussaina Yusuf wadanda aka fi sani da’ yan biyun Shirin Dadin Kowa sun bayyana aniyar su ta yin aure a nan gaba kadan. Jaruman su bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya in da su ke cewa. “Mu a yanzu babban burin mu shi ne nan gaba kadan mu yi aure wannan shi ne abin da ya rage a gare mu domin duk wani suna da a ke yi a cikin harkar fim mun riga mun yi”.Hassana da Husaina Da muka…

Read More

Ba Zan Manta Tagomashin Da Harkar Fim Ta Yi Mini Ba – Safna Maru

Tsohuwar Jaruma a Masana’antar shirya fina-finai ta Kannywwod Kuma Furodusa Sapna Aliyu Maru tace ba zata manta da harkar fim ba domin ita ce ta zamo Silar duk wani abu da ta samu a rayuwar ta. Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Jaridar Dimukaradiyya in da take bayyana cewa. “Magana ta gaskiya duk wanda ya sanni da harkar fim ya sanni, duk da cewar a yanzu na Dade ba na yin fim saboda harkokin da suke gaba na, Amma dai alhamdulillahi harkar fim ta yi mini…

Read More

Duniyar Fina-Finai: Jaruma Maryam Jan Kunne Ta Dawo Fim

A yanzu haka dai tsohuwar jaruma a Masana’antar shirya Fina finan hausa Kanywood Maryam Jankunne ta dawo harkar fim bayan ta shafe tsahon shekaru da ba a ganin fuskarta a cikin Masana’antar. Maryam ta shiga harkar fim a shekarar 2005 daga bisani tayi Aure a shekarar 2008. Jankunne na daya da ga cikin jarumai mata da suka taka rawa a masana’antar Kannywood a shekarun baya kafin tayi Aure. Maryam tayi zamani da irin su Fati Muhammad, Rukayya Dawayya, Rashida mai sa’a, Mansurah Isah da sauran jaruman da suka yi fice…

Read More