Taraba: Mallakar Katin Zabe Shi Ne Cikar Mutum – Garba Pele

Daga: BASHIR ADAMU, JALINGO.

Wani Matashin dan Siyasa a Jalingo fadar gwamnatin jihar Taraba mai suna, Abubakar Inuwa (Garba- Pele) yace Mutum ba zai cika Mutum ba matukar bai Mallaki Katin Zabe na din din ba.

Garba Pele ya bayyana hakane yayin da yake zantawa da Wakilinmu a Birnin Jalingo, Fadar Jihar Taraba. Inda ya hori Al’umma dasu tabbata sun mallaki katin zabe, domin hakane kawai zasu iya zabar nagartattun shugabanni da za su damkawa amanar tafiyar da arzikin Kasarsu.

Da yake tsokaci dangane da Matasa a Siyasa, Inuwa sai yace “Matasa ne ya kamata a ce ke juya akalar Siyasar Duniya, saboda haka yazama wajibi su tsunduma a harkokin Siyasar Kasarnan, amma su hada da sana’anlt yi domin ta haka ne kawai zasu kasance sun zama Matasa nagari.

“Duk dan Siyasar da yace ku yi ta’addanci, to ku fara ta kanshi, kana ku umurceshi da ya sanya ‘ya’yan sa a gaba, “.

A matsayina na Matashi ina cikin Siyasa dumu-dumu, na rike mukamai na Mai taimakawa Gwamna a fannoni daban- daban har sau uku kuma ina kai har a yanzu, amm bai sanyani barin dana’a taba ta asali, na saye da sayar da Raguna, ina kan yi har yau har gobe”.

Garba Pele ya kuma yabawa Gwamna Darius Ishiaku na Jihar Taraba bisa sakewa Jam’iyyar su ta PDP mara na tabbatar da Demokaradiyya tayi aikinta a zabubbukan fidda gwani daya gabata, yana mai cewa mafi akasari Matasa ne suka sami guraben Mukamai da suka hada na Dan Takaran Gwamna, Majalisun Wakilai na Tarayya da na Jiha a Jam’iyyar su a Taraba.

Ya kuma yabawa wadanda suka fadi zabubbukan Fidda Gwanin wa?anda daga bisani suka hakura, suka dauki dangana, kana suka dawo aka hadu domin cigaba da tafiya tare da manufar samun nasarar Jam’iyyar PDP baki daya a Taraba, musamman wanda ya tsaya takarar Majalisar Wakilai na mazabar Tarayya na Kananan Hukumomin Jalingo, Yorro da Zing, Hon. Adam Ibrahim Iman da tawagarsa.

Yana mai bashi tabbacin cewa ko shakka babu samun nasaran Hon. Isma’il Yusha’u Maihanci (Dan Malikin Zing) nasara ce tasu gaba daya, kuma zasu cigaba da fafutukan samun nasarar babban zabe mai zuwa na shekara ta 2023 idan Allah Ya kaimu, da manufa daya na hankoron tallafawa Al’ummah musamman ma Matasan mazabar tasu, dama Jihar baki daya.

Related posts

Leave a Comment