Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya jajanta wa abokan aikinsa da suka kasa samun tikitin takara a karkashin jam’iyyun su a zaben 2023 mai zuwa.
Ahmad Lawan ya sanar da hakan ne yayin da aka dawo zaman majalisar a ranar Talata a jawabinsa na maraba da ‘yan majalisar daga hutun da suka yi.
Lawan, wanda ya nemi tikitin takarar shugabancin kasa da kuma sama da ‘yan majalisar 20 da aka lallasa a zabukan fidda gwanin da aka yi a fadin kasar nan tsakanin watan Mayu da Yuni duk sun dawo majalisar.
Shugaban majalisar dattawan ya yi kira ga sanatocin da aka lallasa a zabukan da kada su sare, su mayar da hankali kan lamurran tsarin siyasa na jam’iyyun su tare da manta sakamakon zabukan fidda gwanin.
Ahmad Lawan ya ce akwai bukatar majalisar ta fifita batun kalubalen tsaron kasar nan kuma ta kara duba gyararrun dokokin zabe. Ya ce yadda aka kammala zabukan fidda gwanin da tsarin shi ya bayyana lamurran da sai an tsaya an duba su a majalisar dattawa.
A yayin jawabi kan sakamakon zabukan fidda gwanin, ya ce, “wasu daga cikinmu sun nemi tikitin sanatoci, wasu abokan aikinmu sun nemi na gwamnonin jihohinsu kuma hudu daga cikinmu sun nemi shugabancin kasa.
“Mun fuskanci sakamako daban-daban, amma a matsayin mu na ‘yan siyasa, tsugune bata kare ba. “Mu cigaba da goyon bayan tsarin siyasa da muka yarda da su. Abokan aikinmu da suka samu nasara, muna muku fatan nasara a zabukan gaba. Sai wadanda ba su samu nasara ba, muna fatan daga yanzu zuwa wani lokaci komai zai daidaita.”
