Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zabe mai zaman kanta ta ?asa INEC, ta sanya ranar yau Litinin domin cigaba da karbar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.
INEC ta ce za a fara karbar sakamakon zaben ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, daidai da ranar 27 ga watan Fabrairu.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ya bayyana hakan a Abuja, ya ce har yanzu basu karbi mafi yawa na sakamakon yadda aka gudanar da zabe a jihohin kasar ba.
Rahotanni daga kasar na cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sanya idanu kan wanda zai maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke gab da kare wa’adi na biyu akan mulki.
A wani labarin kuma jam’iyya mai mulki ta APC, wadda ke marawa Bola Tinubu baya ta lashe zaben jihar Ekiti da yawan kuri’u 201,494, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu yawan kuri’u 89,554, inda jam’iyyar Labour ta Peter Obi ta zo na uku da kuri’u 11,397, yayin da NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso ta samu kuri’u 264.
Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.
Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 20 da jimillar kuri’u 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 343,945 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 10.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku a zaben da jimillar kuri’u 23,283, sai Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 713.
