Arzikin Najeriya Na Dab Da Rugujewa – Sunusi

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), kuma Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya ce, tattalin arzikin Nijeriya yana dab da rushewa.

Sanusi ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya yi na ranar rufe gagarumin taron hannayen jari da aka yi a Kaduna mai taken KADINVEST 6.0, Sanusi ya ce baya ga cewa Nijeriya tana da matsala wurin samar da mai, a yanzu kasuwannin duniya ba su siya.

Ya ce makomar ?asar nan ta dogara ne da tattalin arziki mai dogaro da ilimi, kuma Nijeriya an bar ta a baya a cikin ?asashen Afrika masu dogaro da fasaha da ?ir?ire-?ir?ire.

Sarkin ya jajanta yadda ya kasance ?asar Ghana mai ?aramin tattalin arziki ke zuba hannayen jari a fannin ilimi amma Nijeriya ke zuba kashi 7 na kasafinta a ilimi.

“Mutum takwas kacal a cikin ?ari na ‘yan Nijeriya da suka fara karatun firamare ke kammalawa har zuwa jami’a.”

“A fa?in duniya, aiki ya sauya fasali; kashi talatin zuwa arba’in na ma’aikatan ?asashe masu ?arfin tattalin arziki suna ?o?arin inganta fasahar su zuwa 2030. Amma kuma ta yaya ake samun wannan sauyin? Ilimin fasahar sadarwa da kuma aiki daga gida wanda muka gani yayin annobar Korona.

“Nan ba da da?ewa sakako za su koma yin ayyuka a ?asashe masu yawa kuma wa?anda za su yi aikin za su kasance masu sarrafa sakakon, samar da su ko kuma gyara su.

“A watanni ka?an da suka gabata, ?asar Jamus ta samar da makamashin da ake sabuntawa domin bu?atar dukkan ?asar. A yau muna samun matsala wurin sayar da man fetur a Nijeriya. Ba matsalar samarwa ka?ai ba, har kasuwa babu.

“Don haka, wannan sauyi ne na dole kuma a matsayin na ?asar da ta dogara da man fetur, ya dace abubuwa su sauya.”

“Nijeriya ita ce ?asa ta 114 a duniya cikin kasashen da ke harkar kasuwanci da sana’o’i. Mu ne na ?asa sosai a ?asashen Afrika kamar Kenya, Rwanda da kuma Senegal. A takaice dai muna ?asa ta 14 a kasashen Afrika. Ina ganin ya kamata mu gane wannan, kuma mu duba yadda ?asar tamu take, mu ma daina yekuwar kiran ?asar tamu a matsayin giwar Afrika.

“?asashe kamar irin su Kenya, Ruwanda da Senegal duk suna gaban mu nesa ba kusa ba. Ba ina maganar ma ?asar Afrika ta Kudu ba ne. Abinda za mu kasashe akan ilimi kashi 7 ne kawai cikin ?ari na kasafin ku?in mu a shekara guda kawai, amma ?asar Ghana wadda ba ta da tattalin arziki kamar Nijeriya, kuma ku?in shigar da ?asar ke samu ko kusa bai kai yadda Nijeriya ke samu ba, amma Ghana tana kashe ku?i a fannin ilimi fiye da Nijeriya.

“Sannan abin mamaki ana ta ?auke kamfanoni da masana’antu zuwa Ghana. Mun yi mamakin yadda Shugaban Kasar Ghana ya zama shi ne jagoran shugaban Afrika. Sam ba ma ?o?ari wajen zuba ku?a?e a harkar ilimi da kuma gina al’umma.”

Tsohon Sarkin Kano na 14, ya kiara jaddada cewa akwai bu?atar ?ir?irar fasaha domin matasa wanda zai samar da muhallin havakar tattalin arziki da ci gaba.

Related posts

Leave a Comment