Hukumar za?e ta ?asa ta garga?i jam’iyyun siyasa kan ya?a sakamakon zaben shugaban ?asar da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin ?addamar da bu?e zauren tattara sakamakon za?en shugaban ?asa a Abuja babban birnin ?asar.
Farfesa Mahmood ya ce hukumar INEC ce kawai doka ta ?ora wa alhakin fitar da sakamakon za?en.
“Ina kira ga jam’iyyun siyasa da kafofin ya?a labarai da su ?auki alkaluman sakamakon daga sakamakon da muka sanar, a matsayinmu na wa?anda doka ta ?ora wa alhakin fitar da alkaluman sakamakon za?en”, in ji Farfesa Mahmood.
A jiya Asabar ne dai hukumar ta gudanar da za?en shugaban ?asa da na ‘yan majalisun dokoki na tarayya.
Hukumar na garga?in ne a daidai lokacin da sakamakon za?ukan ke ci gaba da fitowa.
