Shugabancin Kasa: Tinubu Ya Lashe Zabe A Jihar Ekiti

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar jam段yya mai mulki ta APC, wadda ke marawa Bola Tinubu baya ta lashe zaben jihar Ekiti da yawan kuri置 201,494, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu yawan kuri置 89,554, inda jam段yyar Labour ta Peter Obi ta zo na uku da kuri置 11,397, yayin da NNPP Rabi置 Musa Kwankwaso ta samu kuri置 264.

Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.

Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 20 da jimillar kuri置 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam段yyar APC, wanda ya samu kuri置 343,945 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 10.

Dan takarar shugaban kasa na jam段yyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku a zaben da jimillar kuri置 23,283, sai Rabiu Kwankwaso na jam段yyar NNPP ya samu kuri置 713.

Related posts

Leave a Comment