Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar zabe mai zaman kanta ta ?asa INEC, ta sanya ranar yau Litinin domin cigaba da karbar sakamakon zaben shugabancin kasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.
INEC ta ce za a fara karbar sakamakon zaben ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin, daidai da ranar 27 ga watan Fabrairu.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ya bayyana hakan a Abuja, ya ce har yanzu basu karbi mafi yawa na sakamakon yadda aka gudanar da zabe a jihohin kasar ba.
Rahotanni daga kasar na cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabancin kasar, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sanya idanu kan wanda zai maye gurbin shugaba mai ci Muhammadu Buhari, wanda ke gab da kare wa’adi na biyu akan mulki.
A wani labarin kuma jamiyya mai mulki ta APC, wadda ke marawa Bola Tinubu baya ta lashe zaben jihar Ekiti da yawan kuriu 201,494, sai Atiku Abubakar na PDP da ya samu yawan kuriu 89,554, inda jamiyyar Labour ta Peter Obi ta zo na uku da kuriu 11,397, yayin da NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ta samu kuriu 264.
Haka zalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Osun.
Atiku ya samu nasara a kananan hukumomi 20 da jimillar kuriu 354,366 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jamiyyar APC, wanda ya samu kuriu 343,945 kuma ya samu nasara a kananan hukumomi 10.
Dan takarar shugaban kasa na jamiyyar Labour, Peter Obi, ya zo na uku a zaben da jimillar kuriu 23,283, sai Rabiu Kwankwaso na jamiyyar NNPP ya samu kuriu 713.

