Wasanni: An Kori Shugaban Kano Pillars A Firimiyar Najeriya

Hukumar gudanar da gasar Firimiyar Najeriya, LMC ta dakatar da shugaban Kano Pillars, Suraj Yahaya daga shiga harkokin wasanninta nan take.

Hukumar ta fitar da wani jawabi a karshen mako da ya shafi dakatar da shugaban da wasu karin hukunce-hukunce.

An tuhumi Kano Pillars da karya doka ta gudanar da wasannin Firimiya a lokacin da ta buga karawa da Dakkada ranar 23 ga watan Yunin 2022.

A wasan ne shugaban hukumar Pillars, Suraj Yahaya ya ci zarafin mataimakin alkalin wasa Daramola Olalekan.

An kuma ci tarar Kano Pillars da laifin kasa tsawatarwa mahukuntan kungiyar, haka kuma za ta biya naira 250,000 ga mataimakin alkalin wasan da aka ci zarafi.

Haka kuma mahukuntan gasar sun ja kunnen Pillars da cewar za a kwashe mata maki biyu nan gaba, idan ta kara aikata laifi irin wannan.

Za kuma a biya wakilin LMC, Uchenna Iyoke naira 500,000, bayan da wasu kayayyakinsa suka bata, sakamakon hatsaniya a wasan na Kano Pillars da Dakkada.

Haka kuma hukumar gudanar da gasar ta Firimiyar Najeriya ta bukaci a sake duba yadda alkalan wasan tsakanin Kano Pillars da Dakkada kan yadda suka gudanar da aikinsu.

Alkalan sun hada da Ayatu Mohammed, wanda ya yi busa, sai mataimaki na daya, Daramola Olalekan da na biyu, Nura Ali.

A kakar nan Kano Pillars ta ci karo da kalubale da yawa, inda ta buga wasa a Kaduna da Katsina aka mai da ita Kano daga nan ta je Abuja, kafin ta sake komawa Kano.

An kuma ci tarar Pillars naira miliyan tara, sakamakon yamutsi a wasan da ta yi da Katsina United a Kano, daga nan aka yanke mata hukuncin komawa

Related posts

Leave a Comment