Wata Kotun Majistare mai lamba 60, ?ar?ashin Mai Shari’a Tijjani Sale .injibir, ta haramtawa wani matashi hawa doki na tsawon shekara uku.
Matashin, mai suna Abdulsalam Bashir ya gurfana a kotun ne sakamakon ture wata mata da doki har ta samu munanan raunuka.
Bayan hukuncin haramta hawa dokin, al?alin ya yanke wa matashin, ?an unguwar Sabuwar ?ofa da ke a Kano hukuncin zaman gidan yari na shekara ?aya, ko za?in biyan tarar naira dubu 25.
Ya kuma umarci mai laifin da ya biya ku?in magani naira dubu 100 ga matar.
