An tsinci gawar ?an wasan Ghana Christian Atsu a ?ar?ashin ?araguzan gidansa, kamar yadda wakilin ?an wasan ya bayyana, kusan makonni biyu bayan da girgizar ?asa ta afka wa Turkiyya da Siriya.
Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ?ungiyoyin Chelsea da Newcastle.
Tun bayan girgizar ?asar – da ta lalata gidaje da dama a birnin Hayat inda ?an wasan ke zaune – ba a sake jin ?uriyar ?an wasan ba.
Tun da farko ?ungiyarsa ta bayyana cewa an ku?utar da shi da munanan raunuka, to sai dai daga baya, wakilinsa ya tabbatar da cewa ba a ceto shi ba.
“Cikin mummunan tashin hankali da firgice, nake sanar da masu yi wa Atsu fatan alkairi cewa an gano gawarsa da safiyar yau,” kamar yadda wakilinsa Nana Sechere ya bayyana a shafinsa na Tuwita.
“Ina mi?a sakon ta’aziyyata ga iyalai da masoyansa. ina kuma so na yi amfani da wannan dama wajen mika godiya ga duka mutane game da addu’o’i da goyon bayan da suke ba shi”.
