SHUGABAN kwamitin tsangayu na jihar Kaduna, Imam Bukhari Maraban Jos ya maida martani ga masu cewa kada a nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin minista. Shehin Malamin ya yi wannan martani ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023. Imam Bukhari ya ce, “Mun wayi gari, mu ka ga wani rubutu da wani ya yi game da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai. Mu a matsayin mu, mu na martaba gidan Shehu, kuma mu na yarda…
Read MoreDay: July 31, 2023
Babban Gata Da Za A Yi Wa Yara Shi Ne Ba Su Ilimi – Ambasada Musawa
An bayyana cewa babban gata da iyaye za su yi wa ‘ya’yan su shine basu ingantaccen ilimi na addini da na zamani wanda hakan zai sa su zama abin alfahari ga ?asa nan gaba. Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a yayin bikin yaye daliban makarantar Nurul Huda da ya gudana a Arewa House Kaduna, Ambasada Dr Ismail Musawa ya ce ilimi bai da tsada ko da nawa za a kashe wajen neman shi. Dr Musawa ya ?ara da cewa ilimi shi ne tsani guda da ya rage…
Read MoreKungiyar Mahaddata Kur’ani Sun Bukaci A Cire El-Rufai Daga Jerin Sunayen Ministoci
Gamayyar Mahaddata Al-Qur’ani sun yi kira ga Majalisar Dattawa da ta ki Amincewa da sunan Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Sunansa na cikin Ministoci 28 da Shugaban ?asa Bola Tinubu ya mika Domin tantancewa. A yayin zantawa da manema labarai a Bauchi Yau Lahadi, Sheikh Sidi Ali, daraktan ilimi na Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya roki Shugaba Tinubu da ya cire Sunan El-Rufai daga cikin jerin sunayen Ministocin sa. Malamin ya bayar da hujjar cewa na?a El-Rufa’i a Matsayin Minista ya saba wa ka’idojin adalci, daidaito da kuma…
Read MoreBauchi: Shugabannin Izala Sun Nemi Alfarmar A Saki Sheikh Dutsen Tanshi
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci manyan malamai na kungiyar Izala zuwa Bauchi domin nemawa Sheikh Idris Abdulaziz sauki a shari’ar da ake ta zarginsa da tayar da hankalin jama’a. Fintiri tare da shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarenta Sheikh Kabiru Gombe da kuma wani malami mazaunin Kano Sheikh Abdulwahhab sun gana da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad. Babban sakataren yada labarai na Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya tabbatar wa majiyarmu ganawar, inda ya ce gwamnan…
Read MoreBauchi: Shugabannin Izala Sun Nemi Alfarmar A Saki Sheikh Dutsen Tanshi
Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Bauchi na bayyana cewa Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya jagoranci manyan malamai na kungiyar Izala zuwa Bauchi domin nemawa Sheikh Idris Abdulaziz sauki a shari’ar da ake ta zarginsa da tayar da hankalin jama’a. Fintiri tare da shugaban kungiyar Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau da sakatarenta Sheikh Kabiru Gombe da kuma wani malami mazaunin Kano Sheikh Abdulwahhab sun gana da gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad. Babban sakataren yada labarai na Fintiri, Humwashi Wonosikou, ya tabbatar wa majiyarmu ganawar, inda ya ce gwamnan…
Read MoreAn Wayi Gari Da Ganin Hotunan Sunusi Lamido A Fadar Gwamnatin Kano
Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewa an wayi gari an ga an daura hotunan Muhammadu Sanusi II da na Shugaban kasa da Gwamna a gidan Gwamnatin jihar Kano. Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke Sanusi II daga sarautar Kano bayan an yi zaben 2019 Ana rade-radin Basaraken zai sake rike sarautar idan Jam’iyyar NNPP ta kafa gwamnati a Kano. Rahotanni sun bayyana cewa an hangi hotunan Sarkin Kano na 14, Mai martaba Muhammadu Sanusi II a gidan gwamnatin jihar Kano. Wani ‘dan kasuwa mai suna Kabiru…
Read MoreAn Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Badakalar Emefiele
Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na?a wani mai bincike na musamman mai suna Jim Osayande da zai yi bincike a babban bankin Najeriya. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaba Tinubu ya aika wa Obazee, shugaban hukumar masu bayar da rahotannin harkar ku?a?e ta Najeriya. Tinubu ya ce za a binciki CBN da hukumomin da ke da ala?a da bankin ta hanyar amfani da ?wararru da hukumomin tsaro da masu ya?i da rashawa da suka dace…
Read MoreMajalisar Dattawa Za Ta Fara Tantance Ministoci A Yau Litinin
A ranar Litinin din nan ne ake sa ran majalisar dattawan Najeriya za ta fara zaman tantance mutane 28 da Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya mika mata, domin amincewa ya nada su ministoci. Haka kuma ana sa ran shugaban zai aika da wasu karin sunayen kasancewar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya. Daga sunayen da Shugaban kasar ya mika wasu jihohin suna da mutum biyu yayin da wasu ba su da ko daya.…
Read More