Mun Shirya Tsaf Wajen Karbar Kwankwaso – Jam’iyyar NNPP

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jam’iyyar kafin zuwan zaben 2023.

Kamar yadda jam’iyyar ta shaida, nan da ‘yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma sabuwar jam’iyyar ta NNPP.

Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jam’iyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.

Yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban kwamitin zartarwa na NNPP, kuma sakataren jam’iyyar, Ambasada Agbo Major ya ce sun yi taro ne don tattaunawa akan yadda zasu bunkasa jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

“Mu ‘yan kwamitin zartarwa mun saba yin taro irin wannan, kuma muna yin shi lokaci bayan lokaci don tattaunawa akan matsaloli da kuma ci gaban jam’iyya, amma taron mu na yau na daban ne.

“Yanzu haka ‘yan Najeriya suna shirin babban zaben da ke karatowa kuma muna shirin gyara jam’iyyar sannan yanzu haka ‘yan Najeriya suna ta shiga jam’iyyar.

“Abinda zan iya shaida muku shi ne yanzu haka mun yi nisa a tattaunawar da muke yi da Kwankwaso kuma nan da ba dadewa ba zai dawo jam’iyyar NNPP tare da mabiyan sa.”

A cewarsa, jam’iyyar NNPP ba za ta yi maja da wata jam’iyyar ba Ya ce jam’iyyar zata tsayar da Kwankwaso don ya yi takarar shugaban kasa inda yace babu wanda za a ba damar tsayawa takara in banda shi.

Related posts

Leave a Comment