Wasanni: An Bai Wa Everton Hakurin Buga Fenariti

Kungiyar alkalan wasan kwallon kafa ta Ingila ta bai wa Everton hakuri saboda hana ta bugun fenareti a wasanta da Manchester City.

Shugaban kungiyar Mike Riley ya kira kocin kungiyar Frank Lampard ta waya, ya fada masa cewa suna ba kulob din hakuri bisa kuskuren da aka tabka a wasan na ranar Asabar.

City na cin daya ne a Goodison Park a lokacin da dan wasan tsakiyarta Rodri ya taba kwallo da hannu a da’irar gola.

To amma lafari Paul Tierney ya ce ba tabin a zo a gani bane, kuma abokin aikinsa Chris Kavanagh da ke kula da na’urar VAR yace masa bai gamsu cewa tabin ya isa ya zama fenareti ba.

Hakan na zuwa yayin da Everton ke kokarin nisanta kansa daga yan kasa , inda take zaune na 17 a teburin Premier League.

Related posts

Leave a Comment