Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Jamiyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta ce suna kan tattaunawa da tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso akan batun komawar sa jamiyyar kafin zuwan zaben 2023.
Kamar yadda jamiyyar ta shaida, nan da yan kwanaki kadan tsohon gwamnan da tawagar sa za su koma sabuwar jamiyyar ta NNPP.
Dama tun a kwanakin baya aka samu bayanai akan yadda Kwankwaso yake shirin komawa wata jamiyyar don tsayawa takarar shugaban kasa bayan ya soki APC da PDP.
Yayin tattaunawa da manema labarai, shugaban kwamitin zartarwa na NNPP, kuma sakataren jamiyyar, Ambasada Agbo Major ya ce sun yi taro ne don tattaunawa akan yadda zasu bunkasa jamiyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Mu yan kwamitin zartarwa mun saba yin taro irin wannan, kuma muna yin shi lokaci bayan lokaci don tattaunawa akan matsaloli da kuma ci gaban jamiyya, amma taron mu na yau na daban ne.
Yanzu haka yan Najeriya suna shirin babban zaben da ke karatowa kuma muna shirin gyara jamiyyar sannan yanzu haka yan Najeriya suna ta shiga jamiyyar.
Abinda zan iya shaida muku shi ne yanzu haka mun yi nisa a tattaunawar da muke yi da Kwankwaso kuma nan da ba dadewa ba zai dawo jamiyyar NNPP tare da mabiyan sa.
A cewarsa, jamiyyar NNPP ba za ta yi maja da wata jamiyyar ba Ya ce jamiyyar zata tsayar da Kwankwaso don ya yi takarar shugaban kasa inda yace babu wanda za a ba damar tsayawa takara in banda shi.

