Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar a ranar Talata ne Babbar Kotun Tarayya a Jihar ta yi fatali da bu?atar da dakataccen Shugaban Hukumar Kar?ar ?orafe-?orafe da Ya?i da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado.
A ro?on da ya shigar gaban kotun, Riminga ya nemi kotun da ta hana kwamitin bincike da majalisar dokoki ta Kano ta kafa, da kuma hana ?an sanda su bincike shi, tsare shi ko yi masa barazana.
Sannan ya ro?i kotun da ta bada umarnin kowa ya dakata ba tare da ?aukar mataki kan takardun shaidar lafiya na biyu da a ke zargin yayi amfani da su.
Da ta ke yanke ?warya-?waryan hukunci Mai Shari’a Jane Inyang, ta ce kwamitin bincike da aka kafa da kuma jami’an tsaro suna da iko da doka ta basu na su binciki Rimingado.
Inyang ta kuma yanke cewa babu hurumi na jaddada ko yin watsi da hukuncin da kotu mai hurumi iri ?aya ta yi da wacce a ka mi?a wa ?orafi ta yi.
Ta kuma ce kamata ya yi Rimingado ya shigar da ?orafi a kan yan majalisar dokoki a Babbar Kotun Jiha ba ta taraiya ba.
