Harin Jirgin Abuja: An Gagara Cimma Matsaya Tsakanin Gwamnati Da ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar akwai alamu da ke nuna an samu tsaiko a tattaunawar da ke gudana tsakanin gwamnatin tarayya da yan ta’addan da suka farmaki jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris, bayan gwamnati ta ki yarda da bukatun su.

Yan ta’addan na rike da kimanin fasinjoji 100 da suka sace a lokacin harin jirgin kasan, wanda ya afku a Katari hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan sun dana masa bam.

An kashe mutane takwas sannan wasu 26 sun jikkata a yayin da yan bindigar suka budewa jirgin wuta sannan a lokacin ne suka sace mutanen da ke hannunsu a yanzu.

Hukumar kula da jirgin kasan Najeriya ta ce bata samu ji daga fasinjoji 163 da ma’aikatan jirgin bakwai, wadanda ke cikin jirgin kasan a lokacin da aka kai farmakin.

An tattaro cewa maharan sun bukaci a saki kwamandojinsu da masu daukar nauyinsu guda 16 da ke tsare a madadin mutanen da suka sace amma gwamnati bata yarda da hakan ba.

Majiyoyin tsaro sun ce hukumomi na kan tattaunawa da yan ta’addan, yayin da suke amfani da wasu hanyoyi domin ceto wadanda aka sace.

“Gwamnatin tarayya na duba bukatunsu saboda wadanda suka sace, amma gwamnati na taka-tsan-tsan; ba za ta iya cika bukatun yan ta’addan ba, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

A baya dai gwamnati ta saki wasu kwamandoji ‘yan Bindiga sun koma sannan ta’addanci ya sake ta’azzara. “Don haka babu wanda ke duba yiwuwar sakin kwamandojin a yanzu.

An kuma ba yan ta’addan kudi a baya kuma lamarin bai inganta ba. Sakamakon rashin ci gaba a tattaunawar, an tattaro cewa mai yiwuwa yan bindigar su fara neman kudin fansa daga yan uwan wadanda suka sace.

Wasu iyalan sun yi zanga-zanga kan sace yan uwansu sannan sun yi korafin cewa yan ta’addan basu tuntube su ba tun bayan da suka sace su kimanin makonni biyu da suka gabata.

Related posts

Leave a Comment