Mayakan Boko Haram sun kaddamar da sabbin hare-hare a ?auyukan jihar Borno a yayin da ake tsakar gudanar da bikin Kirsimet da na sabuwar Shekara inda suka yi mummunan ta’adi. Sai dai duk da haka dakarun sojin Najeriya basu yi masu ta dadi ba yayinda suka yi musayar wuta da su na tsawon sa’o’i masu yawa, inda aka raba dare ana ba ta kashi. Hakan ya tursasa mazauna kauyukan da abun ya shafa tserewa zuwa saman tsaunuka inda suke kallon fafatawar tsakanin dakarun Sojin Najeriya da miyagu ‘yan ta’addan Boko…
Read MoreCategory: Tsaro
Tsaro
Borno: Boko Haram Sun Kaddamar Da Sabbin Hare-Hare A ?auyuka
Mayakan Boko Haram sun kaddamar da sabbin hare-hare a ?auyukan jihar Borno a yayin da ake tsakar gudanar da bikin Kirsimet da na sabuwar Shekara inda suka yi mummunan ta’adi. Sai dai duk da haka dakarun sojin Najeriya basu yi masu ta dadi ba yayinda suka yi musayar wuta da su na tsawon sa’o’i masu yawa, inda aka raba dare ana ba ta kashi. Hakan ya tursasa mazauna kauyukan da abun ya shafa tserewa zuwa saman tsaunuka inda suke kallon fafatawar tsakanin dakarun Sojin Najeriya da miyagu ‘yan ta’addan Boko…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Shugaban ‘Yan Banga
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a daren ranar Lahadi sun kashe shugaban kungiyar ‘yan sintiri a garin Maigora a karamar hukumar Faskari ta Jihar Katsina, Malam Ummaru Balli. ‘Yan bindigan sun kuma yi awon gaba da mutum takwas yayin harin da suka kai a kauyen Rimi da ke karamar hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina. An gano cewa Mallam Balli ya jagoranci wasu ‘yan sintiri zuwa Rimi domin su taka wa ‘yan bindigan da suka kai hari a Rimi birki a dare da abin ya faru amma Allah cikin…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ango Da Amarya
Da misalin karfe tara na safiyar yau litinin, ‘yan bindiga suka tare hanyar kasuwar Gora, a dai-dai garin Gobirawa da ke Runka, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda Suka kashe wani dattijo, Malam Samaila Sufa, har lahira inda suka sassare shi kuma suka harbe shi sau biyu da kuma jima mutane hudu raunuka. Kuma a ranar asabar suka sace wata amarya da angonta, wanda satin su biyu da aure. Majiyarmu da ba ta bukatar a bayyana sunan ta, ta shaida mana cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar zuwa…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Ango Da Amarya
Da misalin karfe tara na safiyar yau litinin, ‘yan bindiga suka tare hanyar kasuwar Gora, a dai-dai garin Gobirawa da ke Runka, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda Suka kashe wani dattijo, Malam Samaila Sufa, har lahira inda suka sassare shi kuma suka harbe shi sau biyu da kuma jima mutane hudu raunuka. Kuma a ranar asabar suka sace wata amarya da angonta, wanda satin su biyu da aure. Majiyarmu da ba ta bukatar a bayyana sunan ta, ta shaida mana cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar zuwa…
Read MoreKaduna: An Hallaka Shugaban ‘Yan Bindiga Nasiru Kachalla
Mummunan fa?a tsakanin manyan ?ungiyoyin ‘yan bindiga biyu a dokar dajin Birnin Gwari ta Jihar Ka ya yi sanadiyar mutuwar gagarumin ?an bindiga Nasiru Kachalla wanda ya jima yana kisa da garkuwa da mutane a Jihar Kaduna. Kachalla ne wanda ake zargin shine jigon bayan ayyukan ta’addanci da dama a Jihar Kaduna da kewaye, an tabbatar da rashin tausayin da imanin shi ga bayin Allah wa?anda suka fa?a cikin tarkon shi. Ana zargin sa da aikata laifukan garkuwa da da dama ciki harda garkuwa da dalibai da malaman makarantar Engraves…
Read MoreTsige Buhari: Dattawan Arewa Sun Yi Tir Da Kalaman Bishop Kukah
?ungiyar Dattawan Arewa ta fito fili ta nuna rashin jin dadin ta akan sakon Kirsimeti da Shahararren Limamin addinin Kirista Bishop Kukah ya yi, inda ya caccaki gwamnatin Shugaban kasa Buhari. Babban Bishop ?in dake zama a Sokoto yanzu ya zargi Shugaban kasa da son kai, da nuna wariya ta ?abilancin addini, inda ya tabbatar da cewar da wata kabilar ce tayi haka, da Najeriya ta kasance cikin yaki a yanzu. A martanin da kungiyar ta Dattawan Arewa NEF ta fitar ta ce duk wanda baya farin ciki da Gwamnatin…
Read MoreNeja: An Kama Basarake Cikin ‘Yan Bindiga
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya bayyana yadda ‘yan sanda suka cafke dagacin garin Tungan Iliya dumu-dumu tare da mahara a wajen bata-kashi da ‘yan sanda. ‘Yan sanda sun tirke gungun mahara a maboyan su cikin dajin Tunga Iliya, a nan ne fa bayan sun bude musu wuta, suma maharan suna maido wuta, har Allah ya baiwa ‘yan sanda sa’ar fin karfin su. Bayan ‘yan sanda sun yi wa maharan zobe sai suka kutsa cikin dajin canciki inda suke boye, sai ko kwatsam suka iske harda Dagacin…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindiga Sun Sace Pastor Da Matarshi
Wasu ‘Yan Bindiga da ba’a san ko su wanene ba ?auke da manyan makamai sun sace babban Paston Majami’ar‘Pentecostal Fellowship’ dake jihar Kaduna Pastor Emmanuel Bako da matar sa Sandra. ‘Yan Bindigar sun tarke fasto Emmanuel da Matarsa Sandra a filin taro da addu’o’in musamman na Kirsimeti mai suna Albarka camp, Fadan Kagoma, kusa da Kafanchan karamar hukumar Jema’a. Kakakin rundunar’yan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da wannan al’amari, sannan ya kara da cewa ‘Yan Bindigar sun afka wa filin taron ne da wajen karfe 8:30 na dare, ranar…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Cikin Dare A Batsari – Arewa Media Writers
A cikin daren jiya ne ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Watangadiya da Biya (Biya ki kwana) cikin karamar hukumar Batsari. A Watangadiya sun sace mutane da ba mu iya tantance adadin su ba. A Biya kuma wanda baifi nisan kilo mita ukku ba daga matsugunnin sojojin dake Batsari, sun yi harbe-harbe, wanda mafi yawan mazauna Batsari sun ji karar bindigogin su, sannan sun dauki mata kuma ance sun harbi mutum daya, amma dai idan Allah yasa mun samu cikakken yadda abun ya faru zamu kawo maku, kamar yadda…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 18 Da Kashe Biyu
A daren jiya Juma’a Ne, ‘yan bindiga suka kai hare-haren a kauyukan kananan hukumomi Batsari da Faskari da kuma Sabuwa a jihar Katsina, inda suka sace mutane goma sha takwas da kashe Mutum biyu a Batsari har lahira. Majiyarmu ta tabbatar mana cewa a daren jiya, sun zo bisa mashina,dauke da bindigogi, suka je garin Daurawa (Garin Ajiya), da ke cikin karamar hukumar Batsari, inda suka kashe mutane biyu kuma suka sace mutum biyu. Sun je garin Kasai da ke karamar hukumar Batsari, sun sace Mata ukku, yanzu haka suna…
Read MoreKaduna: Mutanen Gari Sun Hallaka ‘Yan Bindiga
Wani rahoto kan tsaro da aka gabatarwa gwamnatin Kaduna a ranar Juma’a, ya nuna cewa mazauna ?ananan hukumomin Sanga da Lere sun yi nasarar kashe ?anbindiga shida a lokuta daban-daban. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce a ranar Alhamis ne wasu ?anbindiga suka kai hari a garin Fadan Karshi dake ?aramar hukumar Sanga, inda suka yi wa wani ?an kasuwa fashi, saidai mutanen garin sun far masu tare da ?one biyu daga ciki har lahira. Kuma dai da yammacin ranar ne wasu ?anbindigar suka…
Read MoreKano: An Dam?e Budurwar Da Ta Tura Wa Saurayinta ‘Yan Fashi
Kotun majistiri mai lamba 18 da ke gyadi-gyadi a jihar Kano ta ki amincewa da bada belin wata budurwa da ake zargin ta aika wa saurayinta yan fashi. Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman a zaman kutun na yau Alhamis ya yi watsi da bukatar lauyoyinta, inda suka nemi a bada belinta da matasan da ake zargin ta aika don afkawa saurayin nata. A kwanakin da suka gabata ne dai aka zargi budurwar mai suna Fatima Umar dake zaune a Dantsinke cikin karamar hukumar Kumbotso da aikawa saurayinta gungun matasa har…
Read MoreKaduna: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Da Kona Buhunan Masara A Kasuwar Giwa
‘Yan bindiga da dama sun rasa rayukan su a yayin harin da suka kawo a yankin Galadimawa dake karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna. An kashe ‘yan bindigan ne a yayin da suka kawo farmaki a kasuwar Galadimawa mai ci mako-mako a yammacin yau Laraba, inda ‘yan banga guda biyu da wasu mazauna garin su biyar suka rasa ransu. Majiyarmu ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun dira kasuwar ne da misalin karfe hudu na yamma inda suka bude wuta kan ‘yan bangan, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar biyu…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Tsoho ?an Shekara 89 Da Yin Gaba Da Matarshi
A dare ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi, suka kai hari a Kauyen Gwammata, da ke cikin karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, inda suka kashe Mai Unguwar garin, Alhaji Ibrahim Mai Bale, dan shekara tamanin da tara da kashe dansa Da’u Ibrahim Mai Bale har lahira kuma suka sace Matarsa, Hajia Duduwa Ibrahim Mai Bale, yar shekara saba’in da daya. Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa da misalin karfe sha daya da rabi na daren jiya, inda gidan Mai Unguwa, aka gwada masu Gidan, ba…
Read MoreA Ceto ‘Yata Kamar Yadda Aka Ceto ?aliban ?an?ara – Mahaifin Leah Sharibu
Mahaifin Leah Sharibu Mista Nathan Sharibu ya fito fili ya koka dangane da cigaba da rike diyarshi Leah Sharibu tsawon lokaci da kungiyar Boko Haram ta yi, inda ya yi kiran da a gaggauta sakin diyar tashi kamar yadda aka sako ‘yan makarantar Kankara daga hannun ‘yan ta’adda. Leah Sharibu na ‘yar shekara 14 lokacin da yan ta’addan Boko Haram suka saceta ranar 19 ga Febrairu, 2018, tare da kawayenta 110 a makarantarsu, GGSS Dapci dake karamar hukumar Yunusari ta jihar Yobe. Tun daga lokacin ta kasance a hannunsu saboda…
Read More‘Yan Adawa Ne Ka?ai Ke Cewa Ba A Samu Tsaro A Najeriya Ba – Garba Shehu
Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ceto daliban Kankara alama ce da ke nuna cewa gwamnatin tarayya a tsaye take wajen ganin ta magance matsalar tsaro. Ya ce hatta wanda ba dangin wadannan yara ba, su yi matukar farin ciki da ceto yaran, kuma ga duk mutane masu tunani me kyau ya kamata su yi farin ciki da hakan. Yace amma akwai wanda ke da matsala masu son saka damuwa a tsakanin al’umma wanda ke shakkun kokarin gwamnatinsu na kawar da matsalar tsaro. Ya bayyana…
Read MoreKatsina: ‘Yan Bindiga Sun Sace Basarake Da Mutane 15
‘Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari a kauyen Kaigar Malamai da ke karamar hukumar Danmusa, a jihar Katsina, inda suka sace mutane goma sha shida ciki har da Maigarin Kaigar Malamai, Kabir Mai Unguwa. Majiyarmu ta tabbatar mana cewa ‘yan bindigar sun zo ne a tsakar daren shekaran jiya litinin, wayewar safiyar jiya talata, sun kwashe tsawon awowi suna harbe-harbe, sun jiwa wasu raunuka. Sun shiga gida-gida suna bincike bayan sun tsorata mu, sun tafi da Mai unguwar garin, sun tafi matan sure shidda da ‘yan mata da…
Read MoreMatsalar Tsaro: Sai Gwamnoni Sun Ajiye Siyasa Kafin Za A Yi Nasara – Salisu Bala
Ambasada Salisu Bala Sulaiman wani mai fashin ba?in al’amurra ya bayyana cewa muddin ana son a samu kawar da matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya sai Gwamnonin Arewa sun kawar da banbancin siyasa a gefe daya, sunzo sunyi abinda ya dace karin a samu natija. Ambasada Salisu Bala ya bayyana hakan ne a shirin DIALOGUE da ake gabatarwa na gidan Talabijin da Rediyo na liberty TV Abuja. Idan ka duba yadda Gwamnanonin Katsina da Zamfara suka hada kansu duk da banbancin siyasar dasu ke dashi musamman kan matsalar garkuwa da…
Read MoreCin Amanar Kasa: Hukumar Kula Da ‘Yan Sanda Ta Kori Manyan ‘Yan Sanda Daga Aiki
Hukumar kula da ayyukan yan sanda (PSC) ta sanar da sallamar wasu manyan jami’an rundunar ‘yan sanda guda hu?u bisa laifukan da suka shafi cin amana da nuna rashin kwarewa a aiki. Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar tare da aika sako zuwa ga manema labarai a ranar Lahadi, a Jihar Lagos. Mr Ani ya ce, hukumar ta ?auki wannan matakin ne yayin wani zaman ganawa da hukumar ta yi ranar Juma’ar da ta gabata. “An sallami babban Sufuritanda (CSP) na…
Read More