Kakakin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ceto daliban Kankara alama ce da ke nuna cewa gwamnatin tarayya a tsaye take wajen ganin ta magance matsalar tsaro.
Ya ce hatta wanda ba dangin wadannan yara ba, su yi matukar farin ciki da ceto yaran, kuma ga duk mutane masu tunani me kyau ya kamata su yi farin ciki da hakan.
Yace amma akwai wanda ke da matsala masu son saka damuwa a tsakanin al’umma wanda ke shakkun kokarin gwamnatinsu na kawar da matsalar tsaro.
Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi inda yace gwamnatin shugaban kasa, Muhammadu Buhari tana da kwararru dake taimaka mata wajan magance matsalar tsaro a kasarnan.
