Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Cikin Dare A Batsari – Arewa Media Writers

A cikin daren jiya ne ‘yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Watangadiya da Biya (Biya ki kwana) cikin karamar hukumar Batsari.

A Watangadiya sun sace mutane da ba mu iya tantance adadin su ba.

A Biya kuma wanda baifi nisan kilo mita ukku ba daga matsugunnin sojojin dake Batsari, sun yi harbe-harbe, wanda mafi yawan mazauna Batsari sun ji karar bindigogin su, sannan sun dauki mata kuma ance sun harbi mutum daya, amma dai idan Allah yasa mun samu cikakken yadda abun ya faru zamu kawo maku, kamar yadda Batsari Mediawhatch ta wallafa a shafinta na Facebook.

Rahoto ya samu kungiyar “Arewa Media Writers” al’ummar yankunan maza da mata, yara kanana, da dattijai suna ta gudun Hijira daga kauyukan su zuwa cikin garin Batsari wasu kuma zuwa cikin garin Katsina, domin samun mafaka.

Muna addu’ar Allah ya kawo mana saukin wannan lamari, ya kawo mana karshen rashin zaman lafiyan da ya addabi yankinmu na Arewa. Amin

Related posts

Leave a Comment