Wani rahoto kan tsaro da aka gabatarwa gwamnatin Kaduna a ranar Juma’a, ya nuna cewa mazauna ?ananan hukumomin Sanga da Lere sun yi nasarar kashe ?anbindiga shida a lokuta daban-daban.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya ce a ranar Alhamis ne wasu ?anbindiga suka kai hari a garin Fadan Karshi dake ?aramar hukumar Sanga, inda suka yi wa wani ?an kasuwa fashi, saidai mutanen garin sun far masu tare da ?one biyu daga ciki har lahira.
Kuma dai da yammacin ranar ne wasu ?anbindigar suka tare hanyar Aboro zuwa Kafanchan har suka harbi wani direba, wanda shima ya buge ?aya daga cikin ?anbindigar har lahira.
Aruwan ya ?ara da cewa jami’an tsaro sun basu rahoton cewa ?anbindiga da suka shigo daga wata jiha ma?wabciya sun far wa ?auyen Domawa da ke ?aramar hukumar Lere, saidai jama’ar ?auyen sun tasar masu inda suka kashe uku daga cikinsu.
