Katsina: ‘Yan Bindiga Sun Bindige Tsoho ?an Shekara 89 Da Yin Gaba Da Matarshi

A dare ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga dauke da manyan bindigogi, suka kai hari a Kauyen Gwammata, da ke cikin karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina, inda suka kashe Mai Unguwar garin, Alhaji Ibrahim Mai Bale, dan shekara tamanin da tara da kashe dansa Da’u Ibrahim Mai Bale har lahira kuma suka sace Matarsa, Hajia Duduwa Ibrahim Mai Bale, yar shekara saba’in da daya.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa da misalin karfe sha daya da rabi na daren jiya, inda gidan Mai Unguwa, aka gwada masu Gidan, ba inda suka zame sai gidan mai unguwa. Suna zuwa sukai yunkurin sace shi yaki yadda, sai harbi, nan take ya rasu, dansa na fitowa suka harbe shi, nan take ya rasu shima. Yan bindiga suka sace matar shi, Hajia Duduwa, ‘yar shekara saba’in da daya, yanzu haka tana hannun su.

An yi zana’idar su da safe a garin Gwammata, da safiyar ranar laraba. Allah ya jikansu da rahama .

Related posts

Leave a Comment