Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar da Abdulrasheed Maina ya gabatar na neman a sake dage shari’arsa domin kara shiri don kare kansa. A zaman kotun na ranar Talatar nan, Alkali Okon Abang ya ce matakin da kotun ta dauka na dage shari’ar tun da farko na daga cikin sassaucinta ne amma Mainan yana kokarin yin wasa da hankalin kotu. Tun da farko lauyan hukumar EFCC Farouk Abdullah ya shaida wa kotun cewa an shirya za a ci gaba da shari’ar ne…
Read MoreCategory: Tattalin Arziki
Tattalin Arziki
Zan Samar Da Fasahar Zamani Ta Da?ile Cin Hanci Da Rashawa A Gwamnati- Pantami
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce sanya sabbin dabarun fasahar sadarwar zamani na digital a dukkanin ayyukan gwamnati babban cigaba ne wajan nasara ga yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati. Ministan ya yi wannan tsokaci ne a taron karawa juna sani na kasa kan yaki da cin hanci da rashawa wanda Code of Conduct Bureau, (CCB) ta shirya tare da tallafin Babban Bankin Najeriya mai taken: “Code of Conduct Bureau: Fighting Corruption For Socio-Economic Development in Najeriya” da…
Read MoreAn Yi Nasarar Dam?e Maina
Jami’an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin. Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar. A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami’an tsaron Najeriya da Nijar. Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ne ta sanar da janye belin Abdulrasheed Maina tare da bayar da umarin a kama shi duk inda aka…
Read MoreAl-Mundahana: Saraki Ya ?ara Fa?awa Komar EFCC
Hukumar EFCC tana zargin Bukola Saraki da laifin wawurar Naira biliyan 12 daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake kujerar gwamna, ta hujjoji da dama. ?aya daga cikin shaidun da hukumar EFCC ta kawo ya bada shaida a gaban kotun tarayya da ke zama a Legas, ya fadi yadda Bukola Saraki ya yi facaka da dukiyar gwamnatin jiha. Olamide Sadiq dake aiki da hukumar EFCC a matsayin mai bincike, ya shaida wa kotu cewa da kudin gwamnatin Kwara Saraki ya saye gidaje a garin Ikoyi. Olamide Sadiq ya…
Read MoreDole Ta Sa Muka Rufe Matatun Mai – Kyari
Babban Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, ya ce an rufe matatun man kasar ne duk da kudaden da ake kashewa na gyaransu saboda fasa bututun mai da barayi suka yi. Hakan na kunshe ne a daftarin kasafin kudin 2021 da Kyari ya gabatarwa da kwamitin majalisar wakilai. Kyari ya ce da gangan aka rufe matatun man saboda ba za su iya ci gaba da aiki ba. Ya ce a halin yanzu, layin bututun mai na Excravos da ake kula wa…
Read MoreTattalin Arziki: Gwamnatin Neja Za Ta Zaftare Albashin Ma’aikata
Gwamnatin Jihar Neja ?ar?ashin jagorancin Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello ta kammala shirye-shirye don yanke albashin ma’aikata a jihar da kaso 50 cikin dari domin rage ra?a?in matsalar tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta. Gwamnatin jihar ta fada ma manyan jami’ai na kungiyar kwadago a wani taro a ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, cewa ba za ta iya ci gaba da biyan kaso 100 na albashin ma’aikata ba daga watan Disamban 2020. An tattaro cewa taron ya samu halartan dukkanin mambobin majalisar zartarwa ta jihar illa Gwamna Alhaji Abubakar…
Read MoreAn Zargi Gowon Da Wawushe Ku?a?en Najeriya Lokacin Barin Mulki
Wani ?an majalisar kasar Birtaniya, ya fito ya na ikirarin cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Yakubu Gowon, ya saci kudin al’ummarsa fiye da yadda ake tunani a yayin ban kwana da Kujerar Shugabancin kasa a shekarar 1976. ?an majalisar ya bayyana wannan ne a gaban wani zaure, inda ya jefi Janar Yakubu Gowon mai ritaya da laifin awon gaba da rabin kudin babban bankin Najeriya a wancan lokaci CBN. Ya ?ara da cewar “Mun san yadda Janar Yakubu Gowon ya yi awon-gaba da rabin dukiyar da ke cikin babban bankin…
Read MoreShiga Kurkuku: Zan ?aukaka ?ara A Yau – Ndume
?an Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisa Sanata Ali Ndume, ya bayyana cewar zai ?aukaka ?ara sakamakon cin zarafin da aka yi mishi ta hanyar kamu da jefa shi Kurkuku da Gandirebobin Kurkukun Kuje a birnin tarayya Abuja suka yi jiya Litinin. Lauyan Sanata Ndume, Barista Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau talata a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, domin tabbatar da ganin adalci ya tabbata akan ?an Majalisar. Lauya Marcel Oru yace ba a ba Ndume damar jin ta bakinsa…
Read MoreAl?ali Ya Bada Umarnin Tura Ndume Kurkuku
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja ta bayar da umarnin ajiye Sanata Ali Ndume a gidan gyara hali Kurkuku. Wannan hukuncin ya biyo bayan Sanatan batan Abdulrasheed Maina, wanda sanatan ya tsaya wa yayin karbar belin sa. A zaman kotun na ranar Litinin, kotun ta umarci a kamo Ndume saboda rashin bayyana Maina wanda aka yanke wa hukunci a kan damfara. Tun bayan bada belin maina ne aka fara wasar buya tsakanin kotun da shi Mainan inda ko a watannin baya sanata Ndume ya bayyana cewar shima…
Read MoreBinciken Magu: Duk Wanda Ya Ci Sai Ya Yi Amai – Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya?i da cin hanci da rashawa a kasar nan, ba zai tsallake kan duk wanda aka bincika aka tabbatar da ya yi ba daidai ba. Kan haka ne Buhari ya ce babu wani wanda ya isa ko ake shakkun hukuntawa a kasar nan, matsawar an same shi da danne dukiyar al’umma. Ya yi wannan bayani ne as lokacin da ya ke karbar rahoton kwamitin Ayo Salami wanda ya binciki Ibrahim Magu kan zargin azurta kai da kuma laifin yi wa kudin da ya kwato…
Read MoreAn ?addamar Da Shirin Tallafawa Matan Karkara Da Jari – Ministar Jin ?ai
Shirin nan na Gwamnatin Tarayya na raba agajin tsabar ku?i ga matan karkara, wato ‘Cash Grant for Rural Women’, yanzu ya fara aiki a yankin kudu-maso-gabashin ?asar nan. Hakan ya biyo bayan ?addamar da shirin wanda Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi a Jihar Ebonyi a ranar Alhamis da ta gabata. A wajen taron ?addamarwar wanda aka yi a tsohon Gidan Gwamnati da ke garin Abakaliki, ministar ta shawarci matan da aka raba wa ku?in da su kashe wannan biya sau ?aya na…
Read MoreNajeriya Za Ta Fara Sayen Fetur Daga Nijar
Gwamnatin Najeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur birnin Zinder. The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar. “Gwamnatin tarayyar Najeriya da Jamhurriyar Nijar ta rattafa hannu kan yarjejeniyar sufuri da ajiyar arzikin man fetur,” ma’aikatar arzikin mai a Najeriya ta bayyana a wani jawabi. Bayan tattaunawa da aka kasance anayi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamdou Issoufou, na tsawon watanni hudu…
Read MoreBuhari Zai Karbi Sakamakon Binciken Magu A Yau
A yau jumma’a ne 20 ga watan nuwanba ake sa ran kwamitin da ya binciki tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu zai mika ruhotansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari. Tun a watan Yuli shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamiti karkashin Ayo Salami domin ya binciki zargin da ke wuyan Mista Ibrahim Magu. Rahotanni daga jaridar Vanguard sun bayyana cewa an ga ‘yan kwamitin Salami a fadar shugaban kasa dauke da tulin takardun binciken da su ka yi. Tsohon Alkalin babban kotun daukaka karar ya fada wa ‘yan jarida cewa…
Read MoreKotu Ta Bada Umarnin Kama Maina
Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin janye belin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban tawagar gyaran fanshon ma’aikata (PRTT) da gwamnati ta rushe. A hukuncin da alkalin kotun, Okong Abang, ya zartar ranar Laraba, ya bayar da umarnin a sake kamo Maina ”duk inda aka gan shi”. Lauyan hukumar EFCC, Mohammed Abubakar, ya ce an bayar da belin Maina a kan kudi miliyan N500 da kuma mai tsaya masa; wanda dole ya kasance Sanata mai ci da zai ajiye miliyan N500 a kotu. Lauyan…
Read MoreGwamnatin Tarayya Za Ta Kar?o Gagarumin Bashi – Ministar Ku?i
Gwamnatin tarayya ta ce tana shirye-shiryen ciwo bashin Dala miliyan 750 daga bankin duniya don farfado da tattalin arzikin jihohin Nijeriya. Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a wajen bikin kaddamar da kwamitin farfado da tattalin arziki bayan barnar annobar korona (N-CARES) a Abuja ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba. A cewar ministar, gwamnatin Nijeriya “tana kokarin ciwo bashin dala miliyan 750 a madadin jihohin, don farfado da tattalin arzikinsu da kuma tallafawa marasa karfi. Dangane da tsadar rayuwa da kuma tasirin COVID-19 a Najeriya, ministar…
Read MoreAn ?ara Farashin Man Fetur Zuwa ?170 A Najeriya
?ungiyar dillalan man fetur IPMAN ta umarci ?a?an ?ungiyar su fara sayar da man fetur daga ?168 zuwa ?170 kan ko wace lita. A ranar Alhamis ne dai kamfanin dillancin albarkatun man fetur na Nijeriya PPMC ya fitar da wata sanarwa yana shwarartar dillalan man su fara sayar da shi daga ?168 zuwa ?170 bayan ya yi bitar yanayin kasuwar man ta watan Nuwamba 2020,kuma farashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’ar nan. A kan haka shugaban ?ungiyar ta IPMAN reshen Kano, wadda ta ?unshi jihohin Kano, Katsina, Bauchi…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Sabunta Karfin Lantarki
Ministan ?asa a Ma’aikatar lantarki Mista Goddy Jedy Agba, ya bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya amince da ?arin ?arfin hasken lantarki, domin bunkasar harkokin kasuwanci Makarantu da Asibitoci a fa?in ?asar. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ?addamar na’urorin lantarki masu nauyin kilowatt 100 masu amfani da hasken rana a yankin ?aramar Hukumar Kiwon da ke jihar Ebonyi. Kamar yadda ya bayyana tsarin sabunta karfin lantarki shine mafita wajen cike gi?in da ake fama da shi da ?arancin lantarki a Najeriya. Ministan ya bayyana wannan tsarin…
Read MoreGwamnatin Tarayya Ta Himmatu Wajen Sabunta ?arfin Lantarki – Ministan Lantarki
Ministan ?asa a Ma’aikatar lantarki Mista Goddy Jedy Agba, ya bayyana cewar Shugaban ?asa Buhari ya amince da ?arin ?arfin hasken lantarki, domin bunkasar harkokin kasuwanci Makarantu da Asibitoci a fa?in ?asar. Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ?addamar na’urorin lantarki masu nauyin kilowatt 100 masu amfani da hasken rana a yankin ?aramar Hukumar Kiwon da ke jihar Ebonyi. Kamar yadda ya bayyana tsarin sabunta karfin lantarki shine mafita wajen cike gi?in da ake fama da shi da ?arancin lantarki a Najeriya. Ministan ya bayyana wannan tsarin…
Read MoreKaduna: Kowane Mazaunin Jihar Zai Dinga Biyan Harajin ?1000
Daga shekara mai zuwa ta 2021, ko wane mazaunin Jihar Kaduna baligi zai dinga biyan kudin haraji Naira dubu daya (?1,000) a kowace shekara. Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADRIS), Dr Zaid Abubakar ne ya sanar da manema labarai hakan a Jihar Kaduna, ya na mai cewa biyan kudin harajin ya samu sahalewar sashi na 9 (2) na dokar garambawul da bunkasa kudaden shiga na jihar Kaduna ta 2020 (Kaduna State Tax Codification and Consolidation Law). Dr Zaid ya ce dokar ta tanadi kowane mazaunin Kaduna baligi…
Read MoreBashin Da Ake Bin Najeriya Zai ?aru Da Triliyan 7.67 A 2021 – Ministar Ku?i
Ministar kudi da tsara tattalin arziki, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa nan da watan Disamba na shekarar 2021 bashin Najeriya zai karu zuwa Naira Tiriliyan 38.68. Ta bayyana hakan ne a yayin da ta gabata a majalisa wajan Kwamitin dake kula da basukan cikin gida dana kasashen waje. Ofishin gwamnatin tarayya dake kula da ciwo bashi ya bayyana cewa a watan Yuni da ya gabata, ana bin Najeriya bashin Tiriliyan 31.009. The cable ta ruwaito Zainab Shamsuna Ahmad na cewa nan da shekarar yanzu bashin dake kan Najeriya jihohi…
Read More