?ungiyar dillalan man fetur IPMAN ta umarci ?a?an ?ungiyar su fara sayar da man fetur daga ?168 zuwa ?170 kan ko wace lita.
A ranar Alhamis ne dai kamfanin dillancin albarkatun man fetur na Nijeriya PPMC ya fitar da wata sanarwa yana shwarartar dillalan man su fara sayar da shi daga ?168 zuwa ?170 bayan ya yi bitar yanayin kasuwar man ta watan Nuwamba 2020,kuma farashin zai fara aiki ne daga ranar Juma’ar nan.
A kan haka shugaban ?ungiyar ta IPMAN reshen Kano, wadda ta ?unshi jihohin Kano, Katsina, Bauchi da Jigawa, Bashir ?an-Mallam ya umarci ?a?an ?ungiyar su fara sayar da man kan sabon farashin, lokacin da yake ganawa da ?an jarida a yau Juma’a.
Ya kuke kallon wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka a halin yanzu?
