An ?addamar Da Shirin Tallafawa Matan Karkara Da Jari – Ministar Jin ?ai

Shirin nan na Gwamnatin Tarayya na raba agajin tsabar ku?i ga matan karkara, wato ‘Cash Grant for Rural Women’, yanzu ya fara aiki a yankin kudu-maso-gabashin ?asar nan.

Hakan ya biyo bayan ?addamar da shirin wanda Ministar Harkokin Jin?ai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta yi a Jihar Ebonyi a ranar Alhamis da ta gabata.

A wajen taron ?addamarwar wanda aka yi a tsohon Gidan Gwamnati da ke garin Abakaliki, ministar ta shawarci matan da aka raba wa ku?in da su kashe wannan biya sau ?aya na N20,000 ga kowaccen su ta hanya mai kyau, musamman wajen ?ara jarin ?ananan sana’o’in da su ke da su.

Ta bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce ta kafa shirin don ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ?angin fatara da yunwa a cikin shekaru goma.

Ta ce: “Sa?on mu a gare su shi ne su yi amfani da wannan ku?i ta hanya mai kyau wajen fara ?ananan sana’o’i ta yadda cikin yardar Allah wannan ku?i zai ru?anya yawan sa har su samu damar kula da kan su da iyalan su.

“Mu na fatan gwamnatin Jihar Ebonyi za ta taimaki wa?annan matan da shawarwari tare da goyon baya da sanin makamar aiki, ta ci gaba da ?ora su a kan hanyar gudanar da sana’ar da kowace mace ta za?a.”

Cikin nasa jawabin, Gwamnan Jihar Ebonyi, Injiniya David Umahi, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari saboda wannan shirin wanda ya ce zai taimaka gaya wajen rage wahalhalun da matan karkara su ke ciki a jihar.

Gwamna Umahi, wanda Mataimakin Gwamna Eric Kelechi Igwe ya wakilta a taron, ya bayyana ziyarar da ministar ta kai da cewa ta zo a kan kari, sannan ya yi al?awarin cewa matan za su fara cin moriyar ku?in jarin da aka ba su nan ba da jimawa ba.

Ya ce, “Wannan babbar rana ce domin rana ce kuma da mutanen Ebonyi su ka tashi daga ?angaren hagu zuwa na dama. Babu wata gwamnati da ta ta?a yi wa mutanen Ebonyi irin wannan.

“Na gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da Minista Sadiya Umar Farouq saboda fito da wa?annan tsare-tsare na cigaban ?asa.

“Mata mutane ne masu himma. In da maza ne su ka samu wannan ku?in, washegari sai ka ji za su yi aure da ku?in.

“Mata ba su ba maza umarni, to amma su kan tabbatar da cewa akwai abinci a gida. Saboda wannan abin alheri, mu na godiya, kuma za mu ci gaba da kawo ?o?on barar mu.”

Haka kuma mataimakin gwamnan ya yi kira ga ministar da ta fito da hanyoyin da za a ri?a sa ido kan shirin don auna yadda matan ke ci gaba da amfana da shi a kasuwancin su ko kuma duk abin da su ka yi da ku?in jarin.

Ana sa ran sama da mata 200 daga ?ananan hukumomi 13 da ke Jihar Ebonyi ne za su amfana daga wannan shiri na Gwamnatin Tarayya mai suna ‘Cash Grant for Rural Women’.

Related posts

Leave a Comment