Babban Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC), Mele Kyari, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, ya ce an rufe matatun man kasar ne duk da kudaden da ake kashewa na gyaransu saboda fasa bututun mai da barayi suka yi.
Hakan na kunshe ne a daftarin kasafin kudin 2021 da Kyari ya gabatarwa da kwamitin majalisar wakilai.
Kyari ya ce da gangan aka rufe matatun man saboda ba za su iya ci gaba da aiki ba. Ya ce a halin yanzu, layin bututun mai na Excravos da ake kula wa kamfanin da shi ne kadai ke cikin koshin lafiya. A cewarsa, babu alfanu a ci gaba da gudanar da matatun, ana kashe musu kudade masu yawa ba tare da ana cin moriyarsu ba.
“Misali, idan mutum zai gudanar da matatun mai a Kaduna da Warri, yana bukatar samar da gangar mai 170,000 a kulla yaumin saboda matatun biyu su yi aiki kasha 70 cikin dari” in ji shi. Kyari ya bayyana cewa a yanzu haka, suna da bututun mai sama da kilomita 5,000 tare da manyan ma’ajin 13, wanda a cewarsa dole a basu kariya sosai don hana ayyukan yan fashi.
“Kuma ina iya fada maku cewa a yau baya ga layin bututun Atlas Cove zuwa Ibadan da kuma na Port Harcourt zuwa Abia, babu ko guda daga cikin wadannan bututun da aka yi wa gyara. “Ba za mu iya tura mai cikin wadannan bututun ba saboda tsufa, amma yawan barnar masu fasa bututun ya zarce tunani,” in ji shi.
Ya ce kimanin naira biliyan 43 aka rasa sakamakon ayyukan barayin mai da masu fasa bututu a watan Janairu da Yunin 2020. Cewa duk wata barayi na fasa bututun mai sau 80. A cewarsa wannan ce ta sa kamfanin ya gwammace ya rika dakon mai daga manyan ma’aijiya zuwa sassan Najeriya.
Ya kara da cewa kamfanin zai kashe biliyan N314.9 a kan ayyuka a 2021 sabanin biliyan 444.75 na 2020. Kyari ya kuma sanar da kwamitin cewa kamfanin ya rasa kudaden shiga da ma wasu ayyukansa sakamakon bullar annobar korona.
Durkushewar tattalin arziki da dokar kulle sun karya farashin mai tare da raguwar hakarsa, baya ga karkata da duniya ta fara yi zuwa ga makamashi na zamani. Raguwar kudaden shiga sun tilasta wa NNPC rage kudaden da take kashewa zuwa kashi 40%, kasancewar ta kasa sauke wasu nauyin da suka rataya a wuyanta na tara kudade da aikace-aikace.
A cewarsa, duk da cewa Najeriya na kokarin kara yawan kudaden shiganta ta bangaren mai, ita ma kamar sauran kasashe ta rungumi amfani da makamashi na zamani. Saboda haka ya roki Majalisar Tarayya ta taimaka ta amince da kudurin dokar man fetur (PIDB).
